Shugaban kamfanin facebook yana alfahari da sanya Hausa a manhajarsa

Shugaban Kamfanin Facebook na duniya, Mista Zuckibercer, wanda shi ne mutum na bakwai a jerin mutanen da suka fi kudi a duniya, kuma shugaban masana’artar  kafar sadarwa ta zumunta na Facebook, Mista Mark Zuckerberg ya kai ziyarar aiki Jihar Legas a ziyararsa ta farko a Nahiyar Afirka, inda ya nuna alfraharinsa da sanya harshen Hausa […]

Shugaban kamfanin facebook yana alfahari da sanya Hausa a manhajarsa
Shugaban kamfanin facebook yana alfahari da sanya Hausa a manhajarsa

Shugaban Kamfanin Facebook na duniya, Mista Zuckibercer, wanda shi ne mutum na bakwai a jerin mutanen da suka fi kudi a duniya, kuma shugaban masana’artar  kafar sadarwa ta zumunta na Facebook, Mista Mark Zuckerberg ya kai ziyarar aiki Jihar Legas a ziyararsa ta farko a Nahiyar Afirka, inda ya nuna alfraharinsa da sanya harshen Hausa a manhajar kamfaninsa..
A sakon da ya rubuta a shafinsa na Facebook ya nuna matukar sha’awarsa da rangadin da ya yi a Legas, kana ya kudiri aniyar koyon abubuwa da dama a Najeriya. Kuma tuni ya fara ganawa da matasa ‘yan Najeriya, masu masana’antun kafafen sadarwa na zamani, domin ya kara musu kwarin gwiwa tare da bunkasa harkokin kasuwancinsa.
Shugaban kamfanin na Facebook ya yi alfahari da sanya harshen Hausa a tsarin manhajar harsunan kamfanin kana ya bada tabbacin yin  amfani da wasu harsunan  Nijeriya da za su biyo baya.
Alƙalumma sun nuna cewa kafar  sadarwar ta fesbuk ce tafi kowace kafar sadar da zumuta  shahara da yawan mabiya a inda take da mutum  biliyan 1.7  a halin yanzu.