Shugaban kamfanin man Rasha ya mutu bayan fadowa ta tagar asibiti

Mutuwar ta shi dai cike take da alamomin tambaya

Shugaban kamfanin man Rasha ya mutu bayan fadowa ta tagar asibiti

Ravil Maganov tare da Shugaban Rasha, Vladimir Putin

Shugaban kamfanin man fetur na biyu mafi girma a Rasha, wato Lukoil, Ravil Maganov, ya mutu bayan ya fado ta tagar wani asibiti da ke Moscow, babban birnin kasar.

Hakan dai ya sa ya shiga jerin manyan ’yan kasuwar kasar da suke mutuwa mai cike da ban mamaki a ’yan kwanakin nan.

Majiyoyi guda biyu sun tabbatar wa da kamfanin dillancin labarai na Reuters cewa kafar yada labaran kasar ta Rasha, Interfax, sun ba da rahoton mutuwar mutumin mai shekara 67 a duniya, kodayake ba a yi karin bayani a kai ba.

“Yau [Alhamis] da safe, Maganov ya fado ta tagar babban asibitin Moscow, sannan ya mutu,” kamar yadda Interfax ya rawaito daga bakin wata majiya.

Sai dai a cewar wata majiya ta ’yan sanda, a zantawarta da jaridar RBC Business Daily, Maganov ya fado ne daga benen mai hawa shida.

Kodayake wani a kamfanin man da yake jagoranta ya ce akwai yiwuwar marigayin kashe kansa ya yi, amma wasu mutum biyu da suka san shi sosai sun ce ba sa tunanin hakan.

Da Reuters ya tambayi ’yan sanda ko za su binciki mutuwar a matsayin abar zargi, sai suka ce sai dai a tambayi Kwamitin Bincike na Kasar.

Sai dai kwamitin shi ma bai amsa tambayar ba a kan kokaci.

Zaɓen Edo: Duk wanda ya kaɗa ƙuri’a ya koma gida ya zauna — ’Yan sanda

Hotunan yadda Zaɓen Gwamnan Edo ke gudana

An buƙaci mazauna Benuwe su yi ƙaura saboda fargabar ambaliyar ruwa

Abubuwan da ya kamata ku sani game da Zaɓen Edo