Shugaban Karamar Hukuma a Kano ya kirkiri manhajar dakile matsalar tsaro

An dai sanya wa mahnajar sunan LURA.

Shugaban Karamar Hukuma a Kano ya kirkiri manhajar dakile matsalar tsaro

Shugaban Karamar Hukumar Ungogo da ke Jihar Kano, Injiniya Abdullahi Ramat ya kirkiri wata manhajar wayar salula ga mazauna Karamar Hukumar don ba su damar mika rahoto ga kowanne irin kalubalen tsaro a yankin.

Ya bayyana haka ne a tattaunawarsa da Aminiya, a Kano, inda ya ce an sanya wa manhajar sunan ‘LURA’ kuma za a iya sauketa a kan wayoyin hannu kai tsaye daga ‘Playstore’.

A cewar Shugaban, da zarar mutum ya sauke manhajar a wayarsa, za ta ba shi damar shiga wajen daukar hoto ko bidiyo a wayarshi, kuma zai iya daukar abin da yake faruwa nan take.

Injiniya Ramat ya kuma ce daga nan ne manhajar za ta tambaya dalilin da yasa ake bayar da rahoto, sannan wurin da mutum yake, domin ta aike da bayanan zuwa ofishin Shugaban Karamar Hukumar.

Daga nan ne shi kuma Shugaban zai kai rahoto ga ’yan sanda ko sauran jami’an tsaro Jihar don daukar mataki a cewarsa.

Har ila yau, a bangaren tsaron dai, Shugaban ya ce ya gina sabon ofishin ’yan sanda a ungwar Rijiyar Zaki da Zango mai dauke da kyamarori da za su lura da waje, wanda za ta iya zuko hoto daga tsawon nisan kilomita biyar.

A karshe sai ya bukaci matasa  da su shiga harkokin siyasa a dama da su domin suna da rawar da za su iya taka wa a cikinta.