Shugaban karamar Hukuma ya dakatar da ginin rijiyar dan takarar jam’iyyar adawa a Ibadan

Shugaban riko na karamar hukumar Kudu maso Yammacin Ibadan, Alhaji Taoreed Adeleke, na jam’iyar APC, ya hana ci gaba da gina rijiyar burtsatse da mai neman takarar gwamna a inuwar jam’iyar PDP a jihar, Mista Seyi Makinde, yake yi, domin amfanin ‘yan kasuwar Aleshinloye da gobara tayi musu barna a cikin watan jiya. Shugaban karamar […]

Shugaban karamar Hukuma ya dakatar da ginin rijiyar dan takarar jam’iyyar adawa a Ibadan
Shugaban karamar Hukuma ya dakatar da ginin rijiyar dan takarar jam’iyyar adawa a Ibadan

Shugaban riko na karamar hukumar Kudu maso Yammacin Ibadan, Alhaji Taoreed Adeleke, na jam’iyar APC, ya hana ci gaba da gina rijiyar burtsatse da mai neman takarar gwamna a inuwar jam’iyar PDP a jihar, Mista Seyi Makinde, yake yi, domin amfanin ‘yan kasuwar Aleshinloye da gobara tayi musu barna a cikin watan jiya. Shugaban karamar hukumar da kansa ya jagoranci wasu mutane zuwa kasuwar ta Aleshinloye dake Ibadan, a  Litinin din makon jiya, inda ya umarci dan kwangilar da ke gudanar da aikin ya tattara nasa ya nasa ya fice daga wurin. Wasu daga cikin ‘yan kasuwan sun nuna bacin ransu da daukar wannan mataki.
daya daga cikin ‘yan kasuwar da aka sakaya sunansa wanda aka gudanar da aikin toshe rijiyar a kan idanunsa, ya shaida wa Aminiya, cewa, “a daidai lokacin da Alhaji Taoreed Adeleke, ya iso cikin kasuwar, ya fara tambayar ko wane ne yake gudanar da aikin gina wannan rijiya. An shaida masa cewa, Mista Seyi Makinde, ne yake yin wannan aiki, domin tausaya wa ‘yan kasuwar da gobara ta lakume musu kadarori cikin watan jiya. Amma a nan take sai shugaban karamar hukumar ya rika fadi a fusace cewa, wannan aiki ne da ya rataya a wuyan karamar hukuma, ba aikin wani daga waje ba. Sai kawai ya umarci dan kwangilar da yake kan aiki ya tattara nasa ya nasa ya bar wurin. Kuma a nan take ya umarci mutanen da yake tare da su da su cike dogon ramin da aka fara hakawa, domin samar da wadataccen ruwa a cikin wannan sashe na kasuwar.”
“Ina ganin yin hakan ya sabawa dimukradiya, domin me zai sa a hana ci gaba da wannan muhimmin aiki gina rijiya da wannan mutumi ya tausaya mana yake yi. Me ya hana tun farko su gina mana irin wannan rijiya domin wadata kasuwarmu da ruwa sai yanzu bayan wani ya fara yin aiki, za su ce aikin na su ne?” inji wannan dan kasuwa.
Da aka nemi jin ta bakin shugaban sashen kayan marmari da gobarar ta kone musu shaguna a kasuwar ta Aleshinloye, Mista Ramon Olabamiji, cewa ya yi “wannan abin bakin ciki ne kwarai da shugaban karamar hukuma da kansa ya jagoranci mutane suka fatattaki masu aikin gina mana rijiya a wannan sashe na kasuwarmu. Da ni da dukkan ‘yan kasuwa maza da mata bamu ji dadin abun da aka aikata mana ba, muna zargin sanya siyasa cikin wannan al’amari wanda babu ruwanmu da siyasa sai kasuwancinmu kawai.”
“Tun farko sai da wannan mutumi wato, Mista Seyi Makinde, ya tallafa mana da kudi Naira miliyan daya kafin ya fara aikin gina mana wannan rijiya. Kuma, ya umarci dan kwangilar ya shimfida bututun ruwa a karkashin kasa zuwa cikin kasuwar ne, amma sai shugaban karamar hukuma ya zo mana da cewa wai, an dakatar da aikin ne domin kaucewa daga hadarin wayoyin lantarki da ake yin aikin a karkashin turakunsu”, inji shugaban.
Da yake amsa wata tambaya, shugaban ‘yan kasuwar ya ce, har yanzu ba su karbi tallafin kudi da Gwamna Abiola Ajimobi ya yi musu alkawari ba. Sai dai ya ce, “mun riga mun kammala bayar da jerin sunayen ‘yan kasuwar da gobarar ta yi wa barna ga wakilan da gwamnan ya hada mu da su.
“Muna fatan gwamnati za ta cika alkawarinta, domin bai gagare ta ba,” inji shi.
Wakilinmu ya tuntubi ofishin shugaban karamar hukumar, sai dai ba a kyale shi ya jiyo ta bakin shugaban ba. A maimakon haka wani jami’i da ya ki ya bayyana sunansa, ya ce, “irin wadannan mutane da suke neman mukamai idanunsu yana rufewa ne wajen tallata kansu, domin sayen jama’a da kudi. Ai bai kamata a fara gudanar da wannan aiki na hakar rijiya, ba tare da neman iznin karamar hukuma ba.”