Shugaban karamar Hukuma ya falla wa Kansila mace mari a Kebbi
Shugaban karamar Hukumar Fakai, Alhaji Musa Rabi’u Jarma ya falla wa Kansila mai wakiltar mazabar Birnin Tudu Rakiya Musa mari a ofishinsa, a lokacin da suke gudanar da zaman Majalisar Kansiloli da Shugaban karamar hukumar a makon da ya gabata. A lokacin da Aminiya ta tuntube ta, Kansila Rakiya ta ce sun nemi su zauna […]

Shugaban karamar Hukumar Fakai, Alhaji Musa Rabi’u Jarma ya falla wa Kansila mai wakiltar mazabar Birnin Tudu Rakiya Musa mari a ofishinsa, a lokacin da suke gudanar da zaman Majalisar Kansiloli da Shugaban karamar hukumar a makon da ya gabata.
A lokacin da Aminiya ta tuntube ta, Kansila Rakiya ta ce sun nemi su zauna da Shugaban karamar Hukumar ne tun tuni, domin irin korafe-korafen da ma’aikata ke yi a kan kin biyan wadansu ma’aikata albashinsu da kuma rage wa wasu albashinsu, da dai makamantansu. “Domin mu Kansiloli ne muke da alhakin duk abin da muka ji na korafe-korafen jama’a, mu za mu zauna da Shugaban karamar Hukuma mu ba da shawara, domin a gyara a duk inda aka samu wani kuskure,” inji ta.
Ta ci gaba da cewa: “A lokacin da suna cikin taro, kowane Kansila ya kawo tasa shawara da kuma korafin da yake da shi amma a lokacin da aka zo kaina domin na yi magana, bayan na gama kawo tawa shawara; ina cikin kawo korafina a kan ya rike albashin matar yayana na watanni hudu, kafin in gama magana sai ya tashi kamar yana yin waya. Sai ya zo kusa da ni, sai kawai na ji ya zabga mani mari a fuska. Daga nan sai na mike tsaye na dauki kujera zan buga masa, sai wadansu Kansiloli suka rirrike ni. Shi kuma sai Sakataren karamar Hukuma da wasu Kansiloli suka rirrike shi, sai ya koma ya zauna.
“Daga nan sai ya fito waje yana cewa yau ya mari Kansila, ya kuma mari banza, saboda idan akwai inda za ta ta fada domin a cire shi sai ta je. Ya ce kuma Kansiloli su ke da alhakin cire Shugaban karamar Hukuma, idan ba su san hanyar cire shi ba shi zai nuna masu ko kuma su rubuta korafinsu zuwa Birnin Kebbi a cire shi.”
Haka kuma Kansilar ta yi korafi da zargin cewa hatta yarinyar da zai aura ya dauke ta aiki kuma duk ya gyara wa ’yan uwanta albashi, ana ba su albashi mai tsoka.
Aminiya ta tuntubi daya daga cikin Kansilolin karamar hukumar, wanda yana daya daga cikin wadanda suke wurin, lokacin da al’amarin ya faru, sai dai ya nemi a sakaya sunansa. Kansilan ya tabbatar wa Aminiya cewa lallai Shugaban karamar Hukumar, Alhaji Musa Rabi’u ya zabga wa Hajiya Rakiya Musa mari a lokacin suna zaman Majalisar Zartawa ta karamar hukumar, inda Kansiloli guda Takwas suka sami damar halartar taron, tare da Sakataren karamar hukumar, wanda shi ne mutum na goma a wajen taron.
Da yake karin bayani, Kansilan ya ce: “A halin gaskiya Shugaban karamar Hukumar bai kyauta ba, domin yaya za a ce Kansila ba shi da ikon yin korafi ko kawo wata magana wadda za ta kawo ci gaban karamar hukuma domin a gyara kura-kuren da ke faruwa? Yaya za a ce Kansila ba ta da wata alfarma da za a saurara mata a matsayinta na Kansila mai wakiltar mazabarta?”
Da ya zo kan batun yadda al’amarin ya faru, Kansilan ya ce: “Daga nan sai muka ce ya yi hakuri, ita kuma tun da ta ce ya yi hakuri bai yi ba, ba ta son neman wata alfarma; tun da ta yi da shi ya kiya. Daga nan tana fadin haka sai ya ta so daga inda yake zaune, ya yi kamar zai fita daga cikin ofis, sai kawai muka ji ya zabga mata mari.”
Aminiya ta tuntubi Shugaban karamar Hukuma Alhaji Musa Rabi’u, domin jin ta bakinsa amma ya ce gwamnati ta nada kwamitin bincike, sai an gama sannan zai yi magana.