Shugaban karamar hukuma ya rasu kwanaki 3 bayan lashe zabe a Kano
Sabon shugaban karamar hukumar ya rasu, kwanaki biyu da lashe zaben karamar hukumar Bebeji.
Sabon zababben Shugaban Karamar Hukumar Bebeji da ke Jihar Kano, Ali Namadi ya rasu, kwana uku bayan lashe zaben kananan hukumomin da aka gudanar a jihar.
Ya rasu ranar Talata da misalin karfe 1 na ranar, kamar yadda mai magana da yawunsa, Ibrahim Tiga ya sanar.
- ’Yan sanda sun cafke mace mai garkuwa da mutane a Kano
- Mahaifin tsohon Gwamnan Kano Kwankwaso ya rasu
A ranar Adabar din da ta gabata ne dai aka gudanar da zaben Kananan Hukumomi a Jihar Kano wanda jam’iyyar APC mai mulki ta lashe dukkanin kujerun ciyamomi 44 da na Kansiloli 484.
Sai dai ya zuwa yanzu ba a bayyana dalilin rasuwar ta sa ba.
A ranar Talata ce dai aka tsara rantsar da su domin kama aiki.
Ibrahim Tiga ya ce za a yi jana’izar mamacin a garinsu, da ke Bebeji, ranar Talata da safe.