Shugaban Karamar Hukumar Akwanga ya rasu bayan ya fadi a wurin taro
Ya yanke jiki ya fadi a lokacin da yake tsaka da jagorantar wani taro a ofishinsa
Shugaban Karamar Hukumar Akwanga ta Jihar Nasarawa, Emmanuel Leweh, ya rasu bayan ya yanke jiki ya fadi a yayin da yake tsaka da jagorantar wani taro a ofishinsa.
Dan uwa ga mamacin kuma dan Majalisar Dokokin Jihar Nasarawa, Samuel Tsebe, ya tabbatar da rasuwar shugaban karamar hukumar.
- Rayuwar Allah-ba-ku-mu-samu muke yi —Kansilolin Arewa
- Daukar Aiki: Ranar Litinin za a saki sunayen mutanen da suka ci jarabawar Sibil Difens
“Yayana (Honorabul Emmanuel Joseph Leweh, Shugaban Karamar Hukumar Akwanga) ya rasu bayan gajeruwar rashin lafiya,” kamar yadda ya sanar.
Wata majiya ta ce Mista Emmanuel Leweh, ya yanke jiki ya fadi ne a lokacin da yake jagorantar taron majalisar gudanarwar karamar hukumar ta Akwanga a ofishinsa ranar Litinin.
A ranar Alhamis 13 ga watan Janairun da muke ciki kuma, Mista Leweh, wanda watansa uku rak a kan kujerarsa, ya ce ga garinku nan a wani asibiti da ake jinyar shi a Abuja.