Shugaban Karamar Hukumar Katcha ta Jihar Neja ya rasu
Allah Ya yi wa Shugaban Karamar Hukumar Katcha ta Jihar Neja, anlami Abdullahi Saku, a hatsarin mota.
Allah Ya yi wa Shugaban Karamar Hukumar Katcha ta Jihar Neja, Danlami Abdullahi Saku, rasuwa a hatsarin mota.
Shugaban karamar hukumar ya gamu da ajalinsa ne a kusa da kauyen Kwakuti da ke kan hanyar Minna zuwa Suleja da yammacin ranar Talata.
Kwamishinan Kananan Hukumomi na Jihar Neja, Muazu Hamidu Jantabo, ya tabbatar da rasuwar Honorabul Danlami Saku a hatsarin.
Ya ce abin ya faru ne a lokacin da marigayin ke tare da wasu mutum biyu a cikin motar da ta yi hatsarin.