Shugaban karamar Hukumar Koko ya yi watsi da zuwa ofis

Al’umman garin Besse, hedikwatar karamar Hukumar Koko-Besse da ke Jihar Kebbi, sun bayyana damuwarsu bisa yadda shugaban karamar hukumarsu, Hon. Shu’aibu Ibrahim Koko da manyan jami’ansa suka yi watsi da zuwa aiki a sakatariya karamar hukumar domin gudanar da ayyukansu na mulki da jama’a. A maimakon haka ma sai ya maida ayyukan nasa zuwa cikin […]

Shugaban karamar Hukumar Koko ya yi watsi da zuwa ofis

Al’umman garin Besse, hedikwatar karamar Hukumar Koko-Besse da ke Jihar Kebbi, sun bayyana damuwarsu bisa yadda shugaban karamar hukumarsu, Hon. Shu’aibu Ibrahim Koko da manyan jami’ansa suka yi watsi da zuwa aiki a sakatariya karamar hukumar domin gudanar da ayyukansu na mulki da jama’a. A maimakon haka ma sai ya maida ayyukan nasa zuwa cikin gidansa a can garinsu, sai dai jefi-jefi ana ganin gilmawarsa akan titi idan zai tafi Birnin Bebbi. 

Wani ma’aikacin karamar hukumar mazaunin garin Besse, inda nan ne hedikwatar karamar hukumar take, wanda ya nemi a sakaya sunansa, ya bayyana wa wakilinmu cewa in banda sakataren karamar hukumar da masinjoji da leburori babu wani mai zuwa wurin aiki sai karshen wata wajen karbar albashi.

Majiyar ta kara da cewa shi kansa shugaban karamar hukumar, Hon. Shu’aibu Ibrahim wanda ya maida ayyukan ofin zuwa farfajiyar gidansa, sai ya shafe mako uku bai leka hedikwatar karamar hukumar ba.

Majiyar ta kara da cewa, baya ma ga kauracewa ayyukan ofis din, haka kuma tunda aka zabe shi da kansilolinsa, babu wani abin Allah-san barka da suka gudanar na azo a gani na cigaban al’ummar yankin, sai dai su yi ta shagalinsu daga can inda suke, amma muddin mutum yana ganinsa, to sai dai ya zo ya tsaya bakin titi idan shugaban yana wuce wa zuwa Birnin Kebbi.

Majiyar ta nuna cewa tunda aka kirkiro karamar hukumar ta Koko-Besse ba a taba samun shugaban da ya yaudari al’ummar yankin Besse da ma kauyukan yankin ba kamar Shu’aibu Ibrahim, bisa rashin karfafa zuwan ma’aikata wurin aikinsa da sauran ayyukan cigaban al’umma.

Akan wadannan zarge-zarge da ake yi wa shugaban da manyan jami’ansa, wakilinmu ya nemi jin ta bakin shugaban karamar hukumar ta waya, amma ya kashe wayar tasa, sannan har zuwa lokacin kammala wannan rahoto bai dawo da amsar sakon tes da aka yi ma sa ba.