Shugaban Karamar Hukumar Lokoja ya rasu ana jajiberin Zaben Kogi

Za a yi jana’izarasa bayan sallar Juma’a sannan a binne gawarsa a makabartar Unguwar Kura.

Shugaban Karamar Hukumar Lokoja ya rasu ana jajiberin Zaben Kogi

Taswirar Jihar Kogi

Allah Ya yi wa Shugaban Karamar Hukumar Lokoja, Honarabul Muhammed Danasabe Muhammed rasuwa a Jihar Kogi.

Aminiya ta ruwaito cewa an tabbatar da rasuwarsa da misalin karfe 4:30 na Asubahin wannan Juma’ar a wani asibiti a Lokoja, babban birnin jihar.

Bayanai sun ce an garzaya da marigayin zuwa asibiti ne bayan ya yanke jiki ya fadi a gidansa.

Wakilinmu ya ruwaito cewa, Danasabe na daya daga cikin ’yan siyasar da ke sahun gaba-gaba wajen halartar taruka a shirye-shiryen zaben gwamnan jihar da za a yi a gobe Asabar.

Wata majiya daga bangaren iyalansa ta ce an mika Danasabe Asibitin Shifa da ke Lokoja bayan ya yanke jiki ya fadi a gidansa cikin dare kafin wayerwar gari Juma’a.

Majiyar ta ce za a yi jana’izarasa bayan sallar Juma’a sannan a binne gawarsa a makabartar Unguwar Kura.

Ya rasu ya bar mahaifiyarsa, mata da kuma ’ya’ya.

Kawo yanzu dai masu makoki da alhini sun yi ta tururuwa a gidan mamacin domin jajanta wa iyalansa.

NLC ta yi watsi da ƙara kuɗin kiran waya da data

DSS ta gurfanar da Mahdi Shehu kan zargin ta’addanci

Sojoji sun kashe mataimakin Bello Turji

Harin ’Yan Fashi: Buni ya jajanta wa ’yan kasuwar Ngalda