Shugaban karamar Hukumar Yaounde ya rantsar da sarkin Ekoudou

A ranar asabar 14 ga watan Disamban Shekara ta 2013, Shugaban karamar Hukumar Yaounde ta biyu Yampen Ousmanou ya rantsar da Mohaman Rabiou Hassan a matsayinshi na Basaraken gargajiya na gundumar Ekoudou ta biyu da ta kunshi bangare guda na anguwar Hausawa a birnin Yaounde. Mohaman Rabiou Hassan, wani matashi ne mai gidan kansa da […]

Shugaban karamar Hukumar Yaounde ya rantsar da sarkin Ekoudou

A ranar asabar 14 ga watan Disamban Shekara ta 2013, Shugaban karamar Hukumar Yaounde ta biyu Yampen Ousmanou ya rantsar da Mohaman Rabiou Hassan a matsayinshi na Basaraken gargajiya na gundumar Ekoudou ta biyu da ta kunshi bangare guda na anguwar Hausawa a birnin Yaounde. Mohaman Rabiou Hassan, wani matashi ne mai gidan kansa da ke da shekaru kusan 34 a duniya.
Ya kuma gaji wannan sarauta ce daga hannun marigayi kawunsa, Alhaji Mouhammadou Rindin, bayan wannan ya danka wa daya daga cikin ’ya’yansa sarautar riko a lokacin da ya kwanta cutar ajali.
Amma kuma bayan rasuwarsa, Hukumomi sun shirya zaben sabon sarki ta hanyar jefa kuri’a ga ‘yan takara da fadawan babban sarki suka jefa. Bayan sakamakon da ya bayyana a take ne Mohaman Rabiou ya samu lashe zaben, a gaban magajin marigayi tsohon sarki. Wannan ya gudana a bara ke nan. Sai kuma a yanzu ne Hukumomi suka ba shi alamun da za su taimaka masa wajen gudanar da sarautar. Wadannan alamun sun hada da kakin sarauta, da kuma dokar da ta bashi damar gudanar da sarauta, hadi da tutar kasa.