Shugaban kasar Afirka ta tsakiya ya yi murabus?
Rahotanni na nuni da cewa, Shugaban riko na Jamhuriyar Tsakiyar Afirka, Michel Djotodia, ya sauka daga mukaminsa tun a ranar Alhamis din da ta gabata. Wannan kuwa ya auku ne a daidai lokacin da rikicin kabilanci da addini ya baibaye kasar.Duk da cewa Ministn Sadarwa na kasar ya karyata labarin yin murabus din, amma wani […]
Rahotanni na nuni da cewa, Shugaban riko na Jamhuriyar Tsakiyar Afirka, Michel Djotodia, ya sauka daga mukaminsa tun a ranar Alhamis din da ta gabata. Wannan kuwa ya auku ne a daidai lokacin da rikicin kabilanci da addini ya baibaye kasar.
Duk da cewa Ministn Sadarwa na kasar ya karyata labarin yin murabus din, amma wani mashahurin mutuma birnin Bangui, Simon Koltoua ya tabbatar da gaskiyar lamarin,l inda ya danganta lamari da mummunar shawar da aka bai wa shugaban kasar kan makamai.
Rahotanni sun yi nuni da cewa, shugaban ya bayar da izinin sayen makamai, wadanda za a biyo da su ta Sudan da Chadi. Ya tabbatar da izinin nasa ne, duk da cewa an kakaba musu takunkumin sayen makamai.
Har zuwa lokacin da Amijniya ta kammala rahotoninta, ba a bayar da sanarwar murabus dinsa daga fada shugaban kasa ba.