Shugaban kasar Bolibiya zai fara wasan kwallo a wani kulob
Wani shahararren kulob din kwallon kafa a Bolibiya (Bolibia) da ke wasa a gasar rukuni na daya da ke kasar mai suna Sport Boys ya samu nasarar daukar shugaban kasar Ebo Morales a matsayin daya daga cikin ’yan kwallon da za su yi masa wasa a badi idan Allah Ya kaimu.Shi dai shugaban kasar dan […]

Wani shahararren kulob din kwallon kafa a Bolibiya (Bolibia) da ke wasa a gasar rukuni na daya da ke kasar mai suna Sport Boys ya samu nasarar daukar shugaban kasar Ebo Morales a matsayin daya daga cikin ’yan kwallon da za su yi masa wasa a badi idan Allah Ya kaimu.
Shi dai shugaban kasar dan kimanin shekara 54 yana da sha’awar wasan kwallon kafa don haka ya yi maraba da amincewar da kulob din yi masa don ya buga masa kwallo a kakar wasa mai zuwa. Shugaban zai rika buga kwallo ne a tsakiyar fili watau Midfielder.
A wata sanarwa da kulob din ya fitar a ranar Talatar nan da ta wuce an nuna shugaban kasar zai rika buga wasa na tsawon mintuna 20 ne kacal a kowane wasa saboda yanayin aikinsa sannan yana da damar ya zabi wasan da yakamata ya buga.
Kulob din ya ce shugaban zai rika karbar albashin Dala 214 kwatankwacin Fam 127 ko kimanin Naira dubu 33.
Shugaban kulob din Sport Boys Mario Cronenbold ya bayyana shugaban kasar a matsayin mai sha’awar wasan kwallon kafa don haka ne ma ya amince da tayin da kulob din ya yi masa na buga masa kwallo a kakar wasa mai zuwa.
Ya ce tuni kulob din ya amince da bai wa shugaban rigar wasa mai dauke da lamba 10 kuma za su aika masa da jadawalin wasannin don ya zabi wadanda yake gani zai samu damar bugawa.
Wani dan siyasa na hannun damar shugaban mai suna Edwin Tupa ya ce shugaban ya yi murna da wannan dama da aka ba shi na yin wasa a kulob din.