Shugaban Kasar Burundi ya rasu

Shugaban kasar Burundi Pierre Nkurunziza ya rasu  yana da shekara 55 a duniya. Gwamnatin Burundi ta sanar da mutuwar Shugaba Pierre Nkurunziza bayan ya yi  fama da bugun zuciya a daren Talata talata, 9 ga watan Yuni. Mutuwar ta Nkurunziza mai shekara 55 na zuwa ne bayan zaben kasar na watan jiya da dan takarar […]

Shugaban Kasar Burundi ya rasu

Shugaban kasar Burundi Pierre Nkurunziza ya rasu  yana da shekara 55 a duniya.

Gwamnatin Burundi ta sanar da mutuwar Shugaba Pierre Nkurunziza bayan ya yi  fama da bugun zuciya a daren Talata talata, 9 ga watan Yuni.

Mutuwar ta Nkurunziza mai shekara 55 na zuwa ne bayan zaben kasar na watan jiya da dan takarar jam’iyyarsa Evariste Ndayishimiye ya samu gagarumin rinjaye wanda zai maye gurbinsa a watan Agusta.

Gwamnatin kasar ta ce a ranar Asabar an kwantar da shugaban gadon asibiti bayan ya fara jin alamun rashin lafiya.

Ya kuma  samu sauki daga baya amma sai a ranar Litinin ciwon bugun zuciya ya same shi, kuma kokarin da aka yi na ceto ransa ya faskara.

Ba mu yanke hukunci kan ƙudirin harajin Tinubu ba — Abbas

Masu garkuwa da mutane na neman N10m kan manoma 6 a Taraba

Hotunan Gobarar Kasuwar Laranto da ke Jos

Kasuwar Laranto da ke Jos ta yi gobara

Tags