Shugaban Kasar Syria da matarsa sun kamu da COVID-19

Rabon da a ga Shguaba al-Assad a bainar jama’a tun a 2020.

Shugaban Kasar Syria da matarsa sun kamu da COVID-19

Bashar al-Assad da matarsa a lokacin zaben kasar. (Daga: abcnews.go.com)

Shugaban Kasar Syria Bashar al-Assad da mai dakinsa Asma sun harbu da cutar COVID-19.

Fadar Shguaban Kasar ta bayyana a ranar Litinin cewa bayan ganin alamun cutar ce Shugaba al-Assad da matar tasa suka yi gwajin.

“Bayan ganin alamun COVID-19 Shugaba al-Assad da matarsa Asma sun yi gwajin PCR kuma sakamakon ya nuna suna dauke da ita.

“Sai dai cutar ba ta yi tasiri sosai ko ta galabaitar da su ba,” inji sanarwar wadda ta ce za su rika aiki daga gida tare da killace kansu na kusan mako uku.

Kasar Syria wadda ta shekara 10 tana cikin yaki na da mutum 1,063 da cutar da kashe daga cikin 16,000 da suka kamu da ita a yankuna da ke karkashin ikon gwamnati.

Boko Haram sun ƙone makarantu a Borno

Har yanzu ’yan bindiga ba su saki matar Manjo Janar Rabe ba

An binne gawar Manjo Janar Rabe a Katsina

Wasu tsiraru ne ke rura matsalar tsaro a Najeriya — Christopher Musa