Shugaban Kenya ya bayyana a kotun Hague
A shekaranjiya Laraba ne Shugaban kasar Kenya Uhuru Kenyatta ya gurfana a kotun Manyan Laifuka ta Duniya (ICC) da ke birnin Hague, inda ya fuskanci zarge-zargen aikata laifukan yaki lokacin tashin hankalin da ya biyo bayan zaben shugaban kasa a shekarar 2007.A lokacin da yake shiga cikin zauren kotun, jama’ar da suka yi dafifi a […]
A shekaranjiya Laraba ne Shugaban kasar Kenya Uhuru Kenyatta ya gurfana a kotun Manyan Laifuka ta Duniya (ICC) da ke birnin Hague, inda ya fuskanci zarge-zargen aikata laifukan yaki lokacin tashin hankalin da ya biyo bayan zaben shugaban kasa a shekarar 2007.
A lokacin da yake shiga cikin zauren kotun, jama’ar da suka yi dafifi a gaban kotun sun barke da shewa. Kodayake, masu aiko da rahotanni sun ce lokacin gudanar da shari’ar, Mista Kenyatta ya kasance cikin natsuwa da annashuwa kafin dage zaman kotun da Mai Shari’a Kuniko Ozaki ‘yar kasar Japan ta jagoranta .
Sai dai shugaba Kenyatta ya musanta zargin, ya kuma bayyana zargin da cewa akwai siyasa a ciki. Kuma ya bukaci kotun da ta yi watsi da karar saboda yadda kotun ta “tsani ’yan Afirka.”
Gabanin isarsa birnin Hague a ranar Talata, shugaban ya sauka daga mukaminsa, inda ya nada mataimakinsa William Ruto a matsayin mukaddashin shugaban kasa. Har ila yau Mista Ruton kansa yana fuskantar tuhuma daga kotun, sai dai ba a bayyana cewa ko shi ma zai bayyana a gaban kotun ba, ko kuma a’a.
Babbar Mai Gabatar da kara ta Kotun Fatou Bensouda, wadda ’yar kasar Gambiya ce, ta ce akwai kwararen hujjoji kan Mista Kenyatta. Ta kuma ce za ta shaida wa kotun bayanan waya da kuma shaidu tara wadanda za su bayyana yadda shugaban ya yi amfani da kudinsa wajen rura wutar tashe-tashen hankulan da suka faru.
Mistsa Kenyatta ya dare karagar mulki ne bayan ya lashe zabe a bara, duk da tarin tuhumce-tuhumcen da kotun take masa. Wasu masu bashin baki kan al’amura sun bayyana cewa wannan na iya zama wani tagomashi a gareshi, inda hakan ke nuni da yadda kasashen duniya suke tsoma baki a al’amuran cikin gidan Kenya.
A shekarar 2009 ma kotun ICC ta fitar da sammaci ga Shugaban Sudan Omar al-Bashir bisa zargin aikata laifukan yaki a yankin Darfur. Kodayake har yanzu shugaban bai kai ga bayyana a gabanta ba.