Shugaban Kenya ya rage wa kansa da ministocinsa albashi
Shugaban kasar Kenya ya bayyana cewa ya dace a rage masa albashi da ma dukkannin ministocin da ke gwamnatinsa, a ci gaba da ake da shirin nan na tsuke bakin aljihu don ganin an rage yawan kudin gudanar da gwamnati.Uhuru Kenyatta ya ce za a rage kashi 20 cikin dari daga albashin da yake karba, […]
Shugaban kasar Kenya ya bayyana cewa ya dace a rage masa albashi da ma dukkannin ministocin da ke gwamnatinsa, a ci gaba da ake da shirin nan na tsuke bakin aljihu don ganin an rage yawan kudin gudanar da gwamnati.
Uhuru Kenyatta ya ce za a rage kashi 20 cikin dari daga albashin da yake karba, hakazalika mataimakinsa. Ministoci kuwa za a rage musu kashi 10 cikin 100 daga albashinsu. Ya kuma ce tafiye-tafiye zuwa kasashen ketare sai wadanda suka zama dole ne.
Shugaban ya yi kira ga ‘yan majalisa kasar da su goyi bayan wannan matakin, ganin cewa ‘yan majalisar na daya daga cikin na sahun farko wajen karbar albashi mai tsoka a nahiyar a Afirka.
A cewar shugaban kudin da ake kashewa kan albashi kawai, ba kanana ba ne “saboda sun tasar ma Dala biliyan hudu da miliyan dari shida (fiye da Naira biliyan dari bawai ke nan) ka ga idan mu ka ci gaba a haka wataran za a wayi gari ba kudin da zasu ragu don gudanar da manyar aiyukan ci gaban kasa, to wa gari ya waya?” inji shi
Wata daya dai bayan zabar shi shugabancin kasar, ya yi alkawarin cewa zai rage albashin dukkannin ma’aikatan gwamnati saboda a samu wadatattun kudin yin aiyukan ci gaban kasa.