Shugaban Koriya ta Arewa ya hana taruka na bikin Kirsimeti
Shugaban Koriya ta Arewa, Kim Jong Un ya fito da wata sabuwar doka da za ta hana duk tarukan da zai kunshi shan giya da kade-kade a lokacin bukukuwan Kirsimeti da na sabuwar shekara a kasar baki daya. Hukumar Leken asirin kasar Koriya ta Kudu ce ta bankado wannan shirin na shugaba Kim Jong. Kafar […]

Shugaban Koriya ta Arewa, Kim Jong Un ya fito da wata sabuwar doka da za ta hana duk tarukan da zai kunshi shan giya da kade-kade a lokacin bukukuwan Kirsimeti da na sabuwar shekara a kasar baki daya.
Hukumar Leken asirin kasar Koriya ta Kudu ce ta bankado wannan shirin na shugaba Kim Jong.
Kafar Yahoo ta ruwaito masana tattalin arziki a kasar suna cewa wannan hanin zai janyo tsaiko da matukar ci baya a harkar tattalin arzikin kasar Koriya ta Arewa a watanni masu zuwa, sannan kuma suka ce zuwa lokacin watan Maris na badi, ‘yan kasar za su iya samun kansu cikin mawuyacin hali sakamakon wannan hanin.
Duk da cewa bikin Kirsimeti ba wani babban biki bane da yake bukatar wani hutu mai muhimmanci a kasar Koriya ta Arewa, akwai wasu ‘yan kasar da suke bin addinin Kirista, kuma suke yi yin bikin Kirsimeti tun a ca baya.
A bara ne dai shugaba Jong Un ya sanar da cewa ya dakatar da bikin na Kirsimeti, inda ya ce a maimakon ‘yan kasar su yi rika yin wannan bikin, gara su yi rika yin bikin ranar haihuwar kakarsa wanda ya kama ranar 24 ga watan Disamba.
Sannan kuma shugaban ya yi kokari matuka wajen ganin cewa ya hana yaduwar bikin Kirsimeti a fadin kasar baki daya tun da dadewa. A shekarun da suka wuce, kasar Koriya ta Kudu mai makwabtaka da kasar ce ta gina wata bishiyar bikin Kirsimeti mai tsawon kafa 30 mai dauke da wuta masu kyalli da daukan hankali a wani tsauni da ke kusa da wani yankin da sojoji suka mamaya da za a iya gani daga kasar Koriya ta Arewa. Wanda hakan ya sa Koriya ta Arewa ta ce ba ta yarda da wannan wutar ba saboda zai iya janyo wata matsala da ba a zata ba.