Shugaban kungiyar makafi a Jihar Yobe ya koka kan lamarin nakasassu
Shugaban kungiyar makafi na Jihar Yobe, Malam Buni Ali ya koka kan yadda gwamnatin jihar ke jan kafa ga harkokin rayuwar nakasassu, musamman ma ’ya’yan kungiyar makafi. Malam Buni ya ce an maida su kamar na baya ga dangi kan abin da ya shafi daukarsu aikin gwamnati, duk da cewar akwai da yawa daga cikinsu […]
Shugaban kungiyar makafi na Jihar Yobe, Malam Buni Ali ya koka kan yadda gwamnatin jihar ke jan kafa ga harkokin rayuwar nakasassu, musamman ma ’ya’yan kungiyar makafi.
Malam Buni ya ce an maida su kamar na baya ga dangi kan abin da ya shafi daukarsu aikin gwamnati, duk da cewar akwai da yawa daga cikinsu da suka yi karatu a manyan makarantun ilmi a cikin jihar da ma wasu sassan kasar nan.
Shugaban ya bayyana hakan ne ga Aminiya yayin wata ganawa a harabar ofishinsa da ke garin Damaturu, bisa ga yadda aka rika yi musu alkawarin daukar ’ya’yan kungiyar aiki, ba a cikawa.
Malam Buni ya ce tsawon lokaci gwamnatin jihar tana alkawari kan daukar wasu mambobinsu da suka kammala makarantun koyon sana’o’i da makamantansu aiki, amma har yanzu shiru, kamar an shuka dusa, lamarin da ya jefa da yawa daga cikinsu cikin matsanciyar matsuwa, su da iyalensu.
Ya ci gaba da cewa a shekarun baya kadan gwamnatin jihar ta dauki wasu mambobinsu aiki, amma kuma aka gaza biyansu hakkokinsu na wata-wata har zuwa yanzu, kuma hakan na iya maida su cikin halin yin bara, alhali gwamnati a kullum na furucin samar wa al’umma aikin yi don kawar da zaman banzan da kan haifar da shiga mummunan yanayi.
Don haka ya bukaci gwamnatin ta tuna wadannan alkawuran ta bullo da hanyar cika su cikin lokacin da ya kamata don a samu sauki.