Shugaban Kungiyar Ohaneze-Ndigbo ta Duniya ya rasu
Farfesa Obiozor, wanda tsohon jakandan Najeriya ga kasashen Amurka da Isra’ila ne, ya rasu ne sakamakon rashin lafiya.
Babban Shugaban Kungiyar Al’ummar Kabilar Ibo ta duniya, Ohaneze-Ndigbo, Farfesa George Obiozor, ya rasu.
Gwamnan Jihar Imo, Hope Uzodinma, ya ce Farfesa Obiozor, wanda tsohon jakandan Najeriya ga kasashen Amurka da Isra’ila ne, ya rasu ne sakamakon rashin lafiya.
A ta’aziyyarsa, ya ce, “A madadin gwamnati da al’ummar Jihar Imo, ni Gwamna Hope Uzodinma, ina sanar da rasuwar danmu, abin alfaharinmj, kuma Babban Shugaban Kungiyar Al’ummar Kabilar Ibo ta Ohaneze-Ndigbo, Farfesa George Obiozor.
“Mashahurin masanin, jakada, kuma dattijo mai kishin kasa Farfesa George Obiozor, ya rasu ne bayan takaitaccen rashin lafiya,” in ji sanarwar da gwamnan ya fitar a ranar Laraba da dare.
Ya ce sanarwar babban rashi ga al’ummar Jihar Imo, yankin Kudu maso Gabas da Najeriya da ma duniya.
A cewarsa nan gaba za a sanar da shirye-shiryen jana’iazar mamacin.
A watan Janairu 2021 ne kungiyar Ohaneze-Ndigbo ta zabi Farfesa George Obiozor a matsayin shugabanta a fadin duniya.
Rasuwarsa a ranar Laraba ta zo ne bayan rade-radin da aka yada a ranar Talata cewa ya kwanta dama.