Shugaban Kwamitin Taron kasa ya nemi gafarar Oshiomhole
Shugaban Kwamitin Bada Shawara kan Taron kasa Sanata Femi Okurounmi ya nemi gafarar Gwamnan Jihar Edo Kwamared Adams Oshiomhole dangane da rashin da’ar daya daga cikin wakilan kwamitin Kanar Tony Nyam mai ritaya wanda ya jagoranci wasu mahalarta taron da aka yi a Benin suka hana Gwamnan gabatar da jawabinsa.A cikin wata wasika da ya […]
Shugaban Kwamitin Bada Shawara kan Taron kasa Sanata Femi Okurounmi ya nemi gafarar Gwamnan Jihar Edo Kwamared Adams Oshiomhole dangane da rashin da’ar daya daga cikin wakilan kwamitin Kanar Tony Nyam mai ritaya wanda ya jagoranci wasu mahalarta taron da aka yi a Benin suka hana Gwamnan gabatar da jawabinsa.
A cikin wata wasika da ya aike wa Gwamnan dauke da sanya hannunsa shugaban ya nanata kudirin kwamitin na bin ka’idojin dimokuradiyya wajen sauke nauyin da aka dora masa inda ya nuna rashin jin dadinsa kan rashin da’ar da daya daga cikin wakilan kwamitinsa ya nuna na hana Gwamnan jawabi a gaban kwamitin.
Ya ce kwamitin zai saurari kowane irin ra’ayi kuma ba zai sake lamuntar rashin da’ar da aka yi a Benin ba.
Idan za a iya tunawa an samu hargitsi a Jihar Edo a wurin sauraron ra’ayoyin jama’a da kwamitin ya shirya a Benin ranar Litinin da ta gabatababban birnin Jihar.
An fara rikicin ne lokacin da Gwamna Oshiomole ke jawabi inda ya ce, “Taron ba ya da amfani domin za a kashe kudin al’umma ne kawai ba tare da an cimma wani abu mai ma’ana ba.”
Kalaman Gwamna Oshiomole ba su yi wa wasu dadi ba, inda Kanar Tony Nyiam ya katse Oshiomhole daga ci gaba da magana. Hakan ne ya janyo hargitsi inda matasa da gwamnatin Jihar Edo ta ce ’yan bangar siyasa ne suka soma iface-iface a cikin zauren, inda mukarraban Gwamna Oshiomhole suka rufa masa baya ya fice daga zauren.
Rahotanni sun ce, ’yan kwamitin sun bukaci Kanar Tony Nyiam ya yi murabus daga cikin kwamitin saboda wannan rikicin da ya faru a Jihar Edo.