Shugaban Ma’aikatan Kano ya yi murabus

A watan Afrilun 2022 ne Ganduje ya naɗa Alhaji Bala a matsayin Shugaban Ma’aikatan na Kano.

Shugaban Ma’aikatan Kano ya yi murabus

Shugaban Ma’aikatan Kano, Alhaji Usman Bala ya yi murabus daga muƙaminsa.

Hakan dai na kunshe ne cikin wata sanarwa da Sakataren Gwamnatin Kano, Dokta Abdullahi Baffa Bichi ya sanar a wannan Larabar.

Sanarwar ta ce Gwamna Abba Kabir Yusuf ya umarci Babbar Sakatariyar Hukumar Ma’aikatan, Hajiya Ma’azatu Isa Dutse ta ci gaba da lura da ayyukan Ofishin har zuwa lokacin da za a naɗa magajinsa.

Ana iya tuna cewa, a watan Afrilun 2022 ne tsohon Gwamnan Kano, Abdullahi Umar Ganduje ya naɗa Alhaji Bala a matsayin Shugaban Ma’aikatan na Kano.

Wata guda da yi masa naɗin, Ganduje ya sake daga likafar Alhaji Bala, inda ya kara masa da mukamin Shugaban Ma’aikatan Fadar Gwamnatin Kano.

Uwa ta jefo jaririnta daga saman bene mai hawa biyu

An yi zanga-zangar kisan ɗalibi a Jami’ar FUDMA da ke Katsina

NNPP ta dakatar da Kawu Sumaila da Ali Madakin Gini

Mun gano inda Bello Turji ya ɓoye —Sojoji