Shugaban Majalisa ya nemi mambobin APC su jingine batun neman mukamai sai…
Shugaban Majalisar Dokokin Jihar Yobe Alhaji Adamu Dala Dogo ya nemi jagorori da mambobin jam’iyyun da suka narke a sabuwar Jam’iyyar APC su yi hakuri da batun neman mukamai da suke yi har zuwa lokacin da za a kammala dukan shirye-shiryen kasa mukaman kamar yadda yake a ka’idar hadewarsu.Shugaban majalisar ya bayyana haka ne a […]
Shugaban Majalisar Dokokin Jihar Yobe Alhaji Adamu Dala Dogo ya nemi jagorori da mambobin jam’iyyun da suka narke a sabuwar Jam’iyyar APC su yi hakuri da batun neman mukamai da suke yi har zuwa lokacin da za a kammala dukan shirye-shiryen kasa mukaman kamar yadda yake a ka’idar hadewarsu.
Shugaban majalisar ya bayyana haka ne a tattaunawarsa da manema labarai dangane da yadda wasu ke zakewa suna kiran kansu shugabannin sabuwar jam’iyyar, inda ya ce masu wannan buri na neman matsayi a cikin sabuwar jam’iyyar su yi hakuri kada su kawo nakasu a sabuwar tafiya da aka fara don samun damar karbe mulki daga hannun Jam’iyyar PDP wadda ta dauki sama da shekara 14 tana gasa wa al’umma aya a hannu.
Ya ce masu cewa ana ba da kudin gudanar da ayyukan raya mazabu kai-tsaye ga ’yan majalisu su sani ba aikin ’yan majalisa ne a ba su kudin gudanar da ayyukan raya mazabunsu ba, hakkin haka na wuyan majalisar zartarwa ne, su aikinsu shi ne yin dokoki da ba da shawarar wuraren da ke bukatar a gudanar musu da ayyukan raya kasa a mazabunsu don neman sahalewar majalisar zartaswa.