Shugaban Majalisa ya rantsar da Okorocha a matsayin Sanata

Shugaban majalisar dattawan Najeriya, Ahmad Lawan, a yau Alhamis ya rantsar da tsohon Gwamnan jihar Imo, Rochas Okorocha, a matsayin Sanata mai wakiltar mazabar jihar Imo ta Yamma. A ranar Talata da ta wuce ne, hukumar zabe mai zaman kanta INEC ta baiwa Okorocha takardar shaida wanda aka yi wata biyu ana jiran baiwa Sanatan […]

Shugaban Majalisa ya rantsar da Okorocha a matsayin Sanata

Shugaban majalisar dattawan Najeriya, Ahmad Lawan, a yau Alhamis ya rantsar da tsohon Gwamnan jihar Imo, Rochas Okorocha, a matsayin Sanata mai wakiltar mazabar jihar Imo ta Yamma.

A ranar Talata da ta wuce ne, hukumar zabe mai zaman kanta INEC ta baiwa Okorocha takardar shaida wanda aka yi wata biyu ana jiran baiwa Sanatan takardar shaidar lashe zaben Sanata daga mazabar Imo.

An tabbatar da Okorocha a matsayin wanda ya lashe zaben ranar 23 ga Fabrairu 2019, kotu ce ta bayar da umarnin cewa hukumar INEC ba tada hurumin rikewa zababben Sanatan takardar shaidar lashe zaben.