Shugaban Majalisar Adamawa ya sha da kyar
Shugaban Majalisar Jahar Adamawa, Hon. Kabiru Mijinyawa ya sha da kyar, inda gwamnan Jahar Adamawa, Muhammadu Umaru Jibrilla Bindow da wasu sarakunan gargajiya suka kai masa dauki. Majalisar ta Adamawa ta tsige wadansu manyan mambobinta hade da mataimakin Kakakin Majalisar, Sunday Peter. Tsige mambobin dai na da alaka da inda wani mamba, Atiku Hayatu wadda […]

Shugaban Majalisar Jahar Adamawa, Hon. Kabiru Mijinyawa ya sha da kyar, inda gwamnan Jahar Adamawa, Muhammadu Umaru Jibrilla Bindow da wasu sarakunan gargajiya suka kai masa dauki. Majalisar ta Adamawa ta tsige wadansu manyan mambobinta hade da mataimakin Kakakin Majalisar, Sunday Peter.
Tsige mambobin dai na da alaka da inda wani mamba, Atiku Hayatu wadda ke wakiltar karamar Hukumar Uba da Gaya ya bayyana gazawar mataimakin kakakin wajen tafiyattar da aikin majalisar kamar yadda ya kamata.
Wani mamba kuma, Abdurrahman Abubakar wadda ke wakiltar karamar hukumar Mubi ta Kudu ya goyi bayan wannan hukuncin da majalisar ta yanke, inda ya ce majalisar ba ta sami shugabancin da ya dace ba.
Mamba Hayatu Uba ya gabatar da sunaye 15 a cikin 25 wadanda mambobin suka sanya hannu, ya ce duk mambobin da suka sanya hannu a wannan takardar da ya gabatar suna bayan cewa majalisar bata sami shugabancin da ya dace ba.
“Ya kamata duk dan majalisar jiha su tafiyartar da harkokin majalisar kamar yadda ya kamata domin idan ba mu magance wadannan matsalolin yanzu ba, a gaba za ta zamo mana babbar matsala”. Inji shi.
An misanya wadanda aka tsige da wasu mambobin kamar su Emmanuel Tsamdu wadda ke wakiltar karamar hukumar Madagali a matsayin mataimakin kakakin majalisar, da Hon. Hassan Barguma wadda ke wakiltar karamar hukumar Song a matsayin mai fada a ji a majalisar da sauransu.
Koda Aminiya tambayi sabon mataimakin kakakin majalisar, Emmanuel Tsamdo game da kai dauki da gwamna da wasu sarakuna suka kai wa kakakin, sai ya ce “Sun zo wajen ne ba don kakakin ba amma sai don wadansu mambobinmu”.