Shugaban Majalisar Jigawa ya barke da kuka yayin mika kasafin bana
Shugaban Majalisar Dokokin Jihar Jigawa Alhaji Adamu Ahmed Sarawa ya barke da kuka lokacin da yake jawabi kan kasafin kudin jihar na bana da Gwamna Sule Lamido ya mika wa majalisar. Shugaban Majalisar wanda ya kasa danne zuciyarsa kan kasafin ban-kwana da Lamido ya mika wa majalisar, ya ce Jihar Jigawa za ta ci gaba […]
Shugaban Majalisar Dokokin Jihar Jigawa Alhaji Adamu Ahmed Sarawa ya barke da kuka lokacin da yake jawabi kan kasafin kudin jihar na bana da Gwamna Sule Lamido ya mika wa majalisar.
Shugaban Majalisar wanda ya kasa danne zuciyarsa kan kasafin ban-kwana da Lamido ya mika wa majalisar, ya ce Jihar Jigawa za ta ci gaba da gode wa Gwamnan saboda “gagarumar sauyin da ya kawo wa jihar a cikin shekara takwas.” Kuma ya bukaci ’yan siyasa su rika gudanar da harkokin yakin neman zabe cikin kwanciyar hankali tare da kaunar juna, kuma ya shawarci jama’a su kiyaye harshensu daga yin kalamai marasa ma’ana.
Gwamna Lamido ya mika wa majalisar gabatar da kasafin Naira biliyan N99 da miliyan 950 don kashewa a bana.