Shugaban majalisar Libya ya yi murabus

A ranar Talatar da ta gabata ne Shugaban majalisar qasar Libya Mohammed al-Megarif ya yi murabus.A makon da ya gabata ne majalisar qasar ta zartar da dokar hana duk wani babban jami’i a lokacin mulkin Moammar Gadhafi sake riqe wani muqami har tsawon shekara 10, wannan dokar ce ta sanya shugaban majalisar yin murabus.A lokacin […]

Shugaban majalisar Libya ya yi murabus
Shugaban majalisar Libya ya yi murabus

A ranar Talatar da ta gabata ne Shugaban majalisar qasar Libya Mohammed al-Megarif ya yi murabus.
A makon da ya gabata ne majalisar qasar ta zartar da dokar hana duk wani babban jami’i a lokacin mulkin Moammar Gadhafi sake riqe wani muqami har tsawon shekara 10, wannan dokar ce ta sanya shugaban majalisar yin murabus.
A lokacin da al-Megarif yake jawabin murabus xin ya ce, yana da yaqinin ’yan majalisar sun zartar da wannan dokar ne sakamakon matsin lamba daga ’yan bindiga. Amma duk da haka ya yanke shawara yin murabus xin don girmama demokuraxiyya.
“Ya kamata komai ya riqa tafiya kamar yadda demokuraxiyya ta assasa, domin hakan ne zai girmama da kuma xaukaka demokuraxiyya.” Daga nan sai ya fara hawaye bayan wani lokaci sai ya ce: “A yanzu ina miqa takardar murabus xina a hannunku, ina buqatar ku yi mini shaida a kan hakan.”
A lokacin mulkin Gadhafi al-Megarif ne jakadan Libya a Indiya a shekarar 1980, kafin daga baya ya zama abokin adawar Gadhafi, hakan ta sanya ya yi gudun hijira, amma bayan an kashe Gadhafi sai ya dawo Libya ya kuma zama shugaban majalisa.
“Ina qara kira cewa yunqurin amfani da qarfin tuwo ko kuma amfani da tsinin bindiga ba za su tava haifar wa demokuraxiyya idanu ba.” Inji shi.
A ranar Talatar ya ce, har yanzu akwai dubban makamai a hannu waxanda suke iqrarin juyin juya-hali. Inda kuma ya ce siyasar qabilanci da tsana da kuma rashin ga maciji tsakanin ‘yan qasar za ta iya ruguza Libya.