Shugaban makaranta ya sa dalibi dauko salula daga masai
An yi kiran a kwace lasisin malantarsa.
An hukunta shugaban wata makarantar karamar sakandare a Afirka ta Kudu kan laifin cin zarafin yara, sakamakon bai wa wani dalibinsa mai shekara 11 umarnin nemo wata wayar salula da ta fada a cikin masai.
Shugaban Karamar Sakandaren Luthuthu da ke Lardin Eastern Cape, mai suna Lubeko Mgandela da aka ba da umarnin ya gurfana a gaban kotu kan tuhumar da ake yi masa ta cin zarafin yara daga bisani an bayar da belinsa.
- Rasuwar Janar Attahiru ta girgiza ni —Na’Allah
- An yi yunkurin kashe Limamin Masallacin Harami yana cikin huduba
A yanzu haka an dakatar da shi daga aiki yayin da ake ci gaba da bincike a hukumance.
Kafofin labarai na kasar suka ruwaito cewa an yi kiran a kwace lasisin malantarsa.
Lamarin ya faru ne bayan da Lubeko ya yi kuskuren jefa wayar salular a cikin shaddar makarantar.
An yi zargin cewa shugaban makarantar ya yi amfani da igiya mai kauri wajen ceto yaron da aka sakaya sunansa daga cikin ramin shaddar, sannan ya bai wa yaron umarnin sanya hannunsa wajen lalubo wayar a cikin kazanta.
Yaron bai samu nasara gano wayar ba, bayan fitowarsa daga shaddar jikinsa ya sharkaf da najasa.
Hakan ya sa ’yan uwansa dalibai suka ta yi masa ba’a, har ya fara jin kunya ya kai ga ya daina zuwa makarantar, kamar yadda iyayensa suka sanar.
Lubeko ya fara biyan yaron ladan Dalar Amurka 3 (kimanin Naira 1,141 da kwabo 50) sannan ya yi wa yaron alkawarin idan ya nemo wayar zai biya shi Dala 13 (kimanin Naira 4,946 da kwabo 50).
Kakar yaron ta bayyana wa Kamfanin Dillancin Labarai na Afirka ta Kudu cewa, ta yi murna da ake bincike kan lamarin.