Shugaban makaranta yi wa karamar yarinya ciki a Katsina

Gidana nake kai ta in ba ta Naira 200 in yi lalata da ita

Shugaban makaranta yi wa karamar yarinya ciki a Katsina

Hoto: Healthyplace

Wani Mataimakin Shugaban Makarantar Sakandare ya shiga bayan ya yi dalibarsa mai shekara 12 cikin shege ta haihu.

Mataikamin Shugaban Makarantar garin Kadandanida da ke Karamar Hukumar Rimi, Ibrahim tukur ya ce yakan ba yarinyar kudi ne a duk lokacin da zai yi lalata da ita.

“Ina kai ta gida na in ba ta N200, N300 zuwa N500 kafin ta yarda in sadu da ita. Ta haifi da na miij ranar Lahadi,” inji malamin wanda ke da mata uku.

Yarinyar mai shekara 12 ta haifi da namiji bayan an yi mata tiyatar CS sakamako cikin da malamin ya yi mata, kamar yadda Rundunar ’Yan Sandan Jihar Katsina ta sanar yayin gabatar da wanda ake zargin.

Kakakin Rundunar, SP Gambo Isah, ya ce, “Idan yarinyar ta je makaranta ne sai ya dauke ta ya kai ta gidansa, kuma yana da aure da mata uku. Sai ka rasa me yake nema daga karamar yarinya ’yar shekara 12? Yanzu ba mu san yadda yadda za ta shayar da jaririn ba.”

An kama masu lalata yara maza

An gurfanar da malamin ne tare da wasu mutum uku da ake zargi da yin lalata da maza uku wadanda ’ya’yan makwabtansu ne.

Bayan makwabtan sun kai wa ’yan sanda rahoto ne aka cafke wadanda ake zargin aka kuma tisa keyarsu zuwa caji ofis.

Hakakazalika an gabatar da wani matashi bisa zargin lalata da karamar yarinya mai shekara biyar a Funtua.

Na yi shekara 20 ina fim amma har yanzu ina fama da talauci — Djimon Hounsou

Tinubu ya tafi Abu Dhabi taro

Lakurawa sun kashe ma’aikatan Airtel 3 a Kebbi

Matashi ya kashe mahaifiyarsa don yin tsafi a Kuros Riba