Shugaban makarantar ya yi wa dalibarsa ‘yar shekara 4 fyade
Ana zargin Abubakar Haruna shugaban makarantar August Nursery and Baby Care and Primary School da ke anguwar Jaba karamar hukumar Sabon Gari da yi wa dalibarsa ‘yar shekara hudu fyade (an sakaya suna) a harabar makarantar. A ranar Juma’a 7 ga Yuni 2019 ne mahaifin yarinyar mai suna Ibrahim Salisu ya kai kara a ofishin […]
Abubakar Haruna Wanda ake zargin da yi wa dalibarsa fyade ‘yar shekara 4
Ana zargin Abubakar Haruna shugaban makarantar August Nursery and Baby Care and Primary School da ke anguwar Jaba karamar hukumar Sabon Gari da yi wa dalibarsa ‘yar shekara hudu fyade (an sakaya suna) a harabar makarantar.
A ranar Juma’a 7 ga Yuni 2019 ne mahaifin yarinyar mai suna Ibrahim Salisu ya kai kara a ofishin ‘yan sanda da ke kasuwar mata da ke Sabon Gari, cewar Shugaban makarantar August ya yi wa ‘yarsa fyade, sai ‘yan sanda suka kama shi.
Bayan ‘yan sandan sun kamo Abubakar Haruna, wanda ake zargin bayan ya amsa laifinsa sai aka tura yarinyar Asibiti domin samun sakamakon binciken likita, Bayan kammala binciken likitocin sun ce an yi sa a baiyi mata rauni sosai ba, kuma sauran binciken da ya shafi sauran gwaje gwaje za a sami sakamako ranar Litinin, a yanzu haka malamin na hannun ‘yan sanda tsare ana jiran sakamako asibitin.