Shugaban Masu Rinjaye da Direban Gwamna sun dambace kan mace a Zamfara

Shugaban Masu rinjaye na Majalisar Dokokin Jihar Zamfara Alhaji Salisu Musa Tsafe da Direban Gwamnan Jihar Alhaji Idris Garba sun dambace kan wata mace mai suna Saratu Garba kaura wadda aka ce suna zargin junansu kan nemanta a tsawon shekaru. Majiyarmu ta ce Alhaji Idris Garba ya jima yana zargin shugaban masu rinjayen da neman […]

Shugaban Masu Rinjaye da Direban Gwamna sun dambace kan mace a Zamfara
Shugaban Masu Rinjaye da Direban Gwamna sun dambace kan mace a Zamfara

Shugaban Masu rinjaye na Majalisar Dokokin Jihar Zamfara Alhaji Salisu Musa Tsafe da Direban Gwamnan Jihar Alhaji Idris Garba sun dambace kan wata mace mai suna Saratu Garba kaura wadda aka ce suna zargin junansu kan nemanta a tsawon shekaru.

Majiyarmu ta ce Alhaji Idris Garba ya jima yana zargin shugaban masu rinjayen da neman matar da zai aura wadda aka ce har ya biya sadakinta kuma ya kai mata lefe, inda aka ce za ta musulunta idan lokacin auren ya yi.
Sai dai wata majiya ta shaida wa wakilinmu cewa shugaban masu rinjayen Salisu Musa ya jima yana nemanta kuma har ya bude mata shago sayar da kayayyakin sawa da kuma shagon sai da abinci, tare da ba ta jarin Naira miliyan biyar da kuma mota.
Wata majiya ta shaida wa wakilinmu cewa kowannensu yana da labarin dan uwansa yana nemanta.
Sai dai a bangaren Saratu Garba ganin yadda take zukar kayayyaki daga Salisu Musa ne, sai ta yi lamo ta ki nuna masa halin da ake ciki tsakaninta da Alhaji Idris don gudun kada ta yi wa kanta sakiyar da babu ruwa, ta toshe wannan hanyar da take samu.
Majiyar ta ce da yake ta fi son Idris, saboda ganin da gaske yake yi zai aure ta, shi ya sa ta amince da shi har ya ba ta dadaki da kayan aure, wanda lokaci kawai ake jira a daura musu aure, kuma wannan ne dalilin da ya sa Idris yake ta kiwonta da kokarin raba ta da duk wanda bai yarda da shi ba ko yake tare da ita.
Da yake zantawa da manema labarai a ofishinsa kan lamarin Shugaban Masu Rinjayen Salisu Musa Tsafe ya bayyana cewa babu abin da yake tsakaninsu sai huldar kasuwanci, kuma ta kira shi ne don ya karbi wasu kudi, amma ya ce yana kan hanya zai same ta a shago. Ya ce bayan ya je shagon ne bai same ta ba, sai ya kirata a waya, ta ki dauka sai daga baya yana bakin shagon sai ga Idris ya ajiye ta a mota, “Bayan ya jiye ta ya tafi ya sake dawowa bayan wani lokaci, nan ya tsaya ya shiga dura mini ashar. Ya ce ashe ni dan iska ne, ni kare ne ban dai tanka masa ba ya tafi,” in jishi.
Ya kara da cewa, “Daga bisani ya sake dawowa ya ce idan na haihu in bi shi, kuma na bi shi, muna haduwa muka shiga zagin juna har ya kawo mini naushi na kauce ni kuma na kai masa naushi na same shi a fuska sai ya cije ni a yatsata kun gani.”
Ya ce bayan an raba su ne sai ya kai karar Direban Gwamnan wajen DPO na Tudun Wada aka kira shi aka sulhunta su.
Da wakilinmu ya tuntubi Direban Gwamna ta waya don jin ta bakinsa sai ya ce ba zai yi magana da ’yan jarida ba. Sai dai wata majiya na ganin wannan ba zai rasa nasaba da sulhun da aka ce an yi a tsakaninsu ba. Majiyar ta ce bayan sulhun sai da aka yi abin a rubuce, don a yi wa tufkar hanci.