Shugaban Masu Rinjaye na Majalisar Dattawa ya fice daga APC
Dan Majalisar Dattawan bai samu ko kira’a daya ba a zaben dan takarar gwamna a APC
Shugaban Masu Rinjaye a Majalisar Dattawa, Sanata Yahaya Abdullahi, ya sauya sheka daga jam’iyyar APC mai mulki zuwa PDP.
Sanata Abdullahi Yahaya daga Jihar Kebbi ya ce fice da jam’iyyar ne bayan ya fadi zaben takarar gwamnan jihar a jam’iyyar APC.
- Duk kuri’ar da ba ta da tambari jabu ce —Jami’an zaben APC
- An yi hayagaga tsakanin Amaechi da ejen a zaben fid-da gwanin APC
- Rikici ya barke tsakanin shugaban APC na Jihar Kano da jami’an tsaro a taron APC
Dan Majalisar Dattawan bai samu ko kira’a daya ba a zaben, sakamakon da ya yi watsi da shi a matsayin wasan yara.
Kakainsa, Muhammad Jamil Gulma, ya sanar cewa, “Shugaban Masu Rinjaye a Majsaliar Dattawa, Sanata Yahaya Abdullahi zai bar Abuja da misalin karfe 9 na safiyar Laraba.
“Zai je Karamar Hukumar Kamba ta Jihar Kebbi inda zai sauya sheka zuwa jam’iyyar PDP a hukumance domin sake neman sake komawa kan kujerarsa.”