Shugaban matasan APC a Gombe ya tsallake rijiya da baya

Wasu batagarin matasa da ba a san ko su wanene ba sun yi yunkurin halaka wani shugaban matasa na APC na Unguwar Herwagana a jihar Gombe, mai suna Shafi’u Idris, ta hanyar lakada masa duka da kuma kwace masa babur. Lamarin ya faru ne da misalin karfe 10 na dare a wata unguwa da ake […]

Shugaban matasan APC a Gombe ya tsallake rijiya da baya

Wasu batagarin matasa da ba a san ko su wanene ba sun yi yunkurin halaka wani shugaban matasa na APC na Unguwar Herwagana a jihar Gombe, mai suna Shafi’u Idris, ta hanyar lakada masa duka da kuma kwace masa babur.

Lamarin ya faru ne da misalin karfe 10 na dare a wata unguwa da ake kira hayin Misau a lokacin da ya gama hira a cikin gari zai tafi gida kawai sai wasu matasa biyu suka bullo a gabansa suka bada masa hodar ibilis suka masa duka suka kwace masa Babur din da yake kai kirar Jenchen Kasea mai lamba ‘Gombe kL 753 YDB’.

Da yake zantawa da wakilinmu bayan an sallame shi a asibiti ya koma gida, Shafi’u Idris ya bayyana masa cewa shi abunda ya sani kawai shi ne yana tafiya gida da dare a daidai kwarin hayin Misau, sai ya ga wasu matasa sun sha gabansa daya ya buga masa sanda a baya daya kuma ya shake shi ya bada masa wata irin hoda da tasa shi maye har suka kwace masa babur. Ya ce a lokacin da suke dukansa ya ji daya daga cikin su ya ce tunda kana shiga rediyo kana zagin mai girma gwamna wata rana sai mun kashe ka.

Shafi’u Idris, ya ce a lokacin da matasan suka masa dukan bai san inda hankalinsa yake ba sanda ya kwana biyu a asibiti yana jinya an daura masa ruwa da allurai shi ne ya samu ya farfado amma da ya yi tsammanin ba zai yi rai ba.

Ganin cewa matasan sun yi awon gaba da Babur din nasa kuma ya ce min sun kai rahoto ofishin ‘yan sanda, hakan ne yasa na nemi jin ta bakin jami’an ‘yan sanda ko sun sami labarin wannan al’amari da ya faru amma lamarin ta ci tura.