Shugaban Namibiya ya lashe kyautar Mo Ibrahim
Shugaban kasar Namibiya mai-barin-gado Hifikepunye Pohamba ya lashe kyautar Mo Ibrahim ta mulki na gari a nahiyar Afirka. Duk shugaban kasar da ya lashe kyautar dai zai karbi kyautar Dala miliyan biyar ( kimanin Naira biliyan daya da miliyan dari ) inda zai dinga karbar Dala dubu 200 a kowace shekara har tsawon shekara 10. […]
Shugaban kasar Namibiya mai-barin-gado Hifikepunye Pohamba ya lashe kyautar Mo Ibrahim ta mulki na gari a nahiyar Afirka.
Duk shugaban kasar da ya lashe kyautar dai zai karbi kyautar Dala miliyan biyar ( kimanin Naira biliyan daya da miliyan dari ) inda zai dinga karbar Dala dubu 200 a kowace shekara har tsawon shekara 10. Sai dai an kwashe shekaru hudu a jere ba a samu shugaban da ya lashe kyautar ba saboda, a cewar masu bayar da ita, ba a samu shugaban wata kasa a Afirka ba da ya gudanar da mulki na gari a cikin shekarun.
Mista Pohamba mai shekara 79, tsohon dan tawaye ne wanda ya yi fafutikar ganin kasarsa ta samu ‘yancin-kai, kuma ya yi wa’adi biyu na shugabancin kasar kawai.
An fara zabensa shugabancin kasa ne a shekarar 2004, sannan aka sake zabensa a shekarar 2009. Mista Hage Geingob shi ne mutumin da aka zaba domin maye gurbin Mista Pohamba, bayan zaben da ya lashe.
A shekarar 2009, an bayar da sunayen tsohon Shugaban kasar Afirka ta Kudu Thabo Mbeki da tsohon Shugaban Najeriya Olusegun Obasanjo da kuma tsohon Shugaban Ghana John Kufor, amma a cikinsu ba a samu wanda ya cike sharuddan lashe kyautar ba.