Shugaban NHIS da aka dakatar ya dawo bakin aiki
Shugaban Hukumar Inshorar Lafiya ta Najeriya (NHIS), Farfesa Usman Yusuf, wanda aka dakatar daga mukaminsa bisa zargin cin hanci da rashawa ya dawo bakin aikinsa a yau Litinin. Masu fada aji na Hukumar ne suka bayar da umarnin dakatar da Farfesa Yusuf har sai an kammala binciken tuhumar da ake yi masa. A yau Litinin […]
Shugaban Hukumar Inshorar Lafiya ta Najeriya (NHIS), Farfesa Usman Yusuf, wanda aka dakatar daga mukaminsa bisa zargin cin hanci da rashawa ya dawo bakin aikinsa a yau Litinin.
Masu fada aji na Hukumar ne suka bayar da umarnin dakatar da Farfesa Yusuf har sai an kammala binciken tuhumar da ake yi masa. A yau Litinin dai Farfessan ya koma ofishinsa dake yankin Utako Abuja ne tare da jami’an tsaro.