Shugaban Nijar ya karrama ni saboda koya wa ‘yan kasar sana’ar fim – Nasiru A dorayi
Nasiru A dorayi tsohon mai daukar hoto ne a masana’artar fim wanda ya shahara, inda a kwanakin baya ne shugaban kasar Nijar ya karrama shi. A hirar da ya yi da Aminiya ya shaida yadda ya kai ga samun wannan lambar yabo da fadi tashin da ya sha a masana’ar fim Aminiya: Ko za ka […]
Nasiru A dorayi tsohon mai daukar hoto ne a masana’artar fim wanda ya shahara, inda a kwanakin baya ne shugaban kasar Nijar ya karrama shi. A hirar da ya yi da Aminiya ya shaida yadda ya kai ga samun wannan lambar yabo da fadi tashin da ya sha a masana’ar fim
Aminiya: Ko za ka gabatar da kanka?
Sunana Nasiru Abubakar dorayi, an haife ni a garin Sakkwato a karamar Hukumar Raba, amma a Jihar Kano na girma na yi karatun Firamare da Sakandare sannan na halarci Jami’ar Bayero, inda na yi karatun difuloma a fannin sadarwa, wato “Mass communication,” sannan na yi kwasa-kwasai da dama.
Aminiya: Ya aka yi ka samu kanka a sana’ar ɗaukar hoto mai motsi?
dorayi: Tun da farko sana’ar da na taso na sani ke nan wato daukar hoto nai motsi ko bidiyo kobaraj (Coberage), domin tun ina dan shekara 15 nike yin sana’ar, a wannan lokacin ba a shirin wasan film kamar yadda ake yi a yanzu, sai dai muna yin sana’ar ne a wajen daurin aure da bukukuwa irin na suna ko maulidi ko makamantan haka. A wannan lokacin akwai mai gidana dana fara koyon aikin a wajensa wani mutumin kasar Ghana Abdura’uf, wanda yake da babban bidiyo kulob a Kano. A lokacin da aka soma shirya fina-finan Hausa a shekarar 1990 sai na komo wannan bangare nan na fara aiki da iyayen gidana su Abdullahi Baba da Cediyar gurasa da Ado Ahmad gidan Dabino ta wajen su ne na tsunduma cikin harkar daukar hoto na fina-finan Hausa.
Aminiya:Wacce gudunmawa wannan sana’a ta daukar hoto ke bayarwa a harkar fim?
dorayi: Alal hakika a duk inda ake shirya fim a duniya in babu mai daukar hoto mai motsi to babu shirin film dinma gaba daya ko a ina ne, domin sai da mai daukar hoto ne fim zai hadu har jama’a su kalla.
Aminiya: Wane tsari mutum zai bi don ya zama kwararen mai daukar hoto a masana’artar fim?
dorayi: Muna da kungiyar masu daukar hoton fina-finai a matakin kasa, tsarin shi ne idan mutum yazo ya ce yana so ya koyi sana’ar zai je ya samu kungiya ya yi rijista sai kungiya ta nemi wanda ya dace ta hada shi da shi ya koya masa aikin, a haka zai dinga tafiya da shi yana koya masa a gida ne ko in an fita aiki. To haka in mutum in ya mayar da hankali sai ka ga ya iya a aikace-aikace daga nan sai mu bai wa mutum shawara ya je makaranta ya koya a karance, ta haka ne mutum zai samu kwakkwarar takardar shaida ko da wani kamfani ya dauke shi aiki ko kuma gwamnati ka ga zai samu alfanun takardun.
Aminiya:Ko aikinka ya takaita a masana’antar fim din Hausa na nan ƙasar ne kawai ?
dorayi: Baya ga masana’antar fim din Hausa ina yi wa ‘yan fim din Turanci aiki wadanda aka fi sani da Najeriyan fim sannan na je kasashen Afirka da dama, inda na yi aiki cikinsu akwai kasar Ghana da Mali , na je Najar sai Togo da dai sauran su. Kuma a nan kasar babu jihar da ban je na yi aiki ba, yau shekaru 26 ina cikin masana’artar fim. A baya bayan nan ma akwai wani fim da muka shirya a kasar Nijar mai suna Orisha; fim ne da ya kunshi harsuna huɗu, a cikinsu akwai Hausa da Turanci da Suwahili da Faransanci. A kan wannan fim din sai da Shugaban kasar Nijar Muhammad Yusif ya ba ni lambar yabo, saboda irin bajintar da muka yi domin mun yi aiki ne na watanni biyu a wannan tsawon lokacin ne muka debi mutane 10 ‘yan kasar Nijar muka koya musu aikin, har suka ƙware a harkar fim kafin mu bar garin. Da wannan fim din ƙasar Nijar ta lashe gasar wani bikin fina-finai na kasar Afirka, wanda aka gudanar a kasar Togo. Shi wannan fim din da muka shirya shi ya bai wa ƙasar Nijar damar lashe wannan gasar.
Aminiya: Ko za ka fada mana fitattun fina-finan Hausa da ka dauki hoton aikin su?
dorayi:Wadanda zan iya tunawa da sunayensu kasancewar ba ni na shirya ba, su ne kamar haka a da can akwai fim din Bakandamiyar rikicin duniya, sai nasan A rina Hodijan, sai irin su Aliya da dai da sauransu da dama. Bayan nan akwai aikin da na yi wa Mai martaba Sarkin Sasa Sardaunan Yamma Malam Haruna mai Yasin. Mun yi aikin ne a zamanin mulkin ‘Yar aduwa a lokacin sai da na shiga daukacin jihohin Kurmi 17 na zanta da daukacin sarakunan jihohin Kurmi, domin a karkashinsa suke. Sannan a wannan aikin mun zanta da tsohon Shugaban kasa Janar Ibarahim Babangida da tsohon Gwamnan Neja Babangida Aliyu da Gwamna Bafarawa na Sakkwato a wancan lokacin da na Jihar Katsina, Wato Gwamna Shema sannan muka zanta da hakimin mahaifar sardaunan Yamman da ke Jihar Katsina a wannan aiki sai da na shafe wata 4 a Kurmi, yau ina Legas gobe ina Abekuta jibi ina Ore gata ina Enugu, a haka muka yi ta yi na karade jihohin Kurmi kafataninsu. Kasancewarsa hamshakin Basarake ne mai jajircewa bisa lammuran ‘yan Arewa a Kurmi.
Aminiya: A kwanankin baya Gwamnatin tarraya ta yi yunkurin gina alkaryar fim wane alfanu kake gani za a samu da ba a soke shirin ba?
dorayi:Alhamdulilahi wannan abu da Allah ya kawo mana shi, sai kuma wani abu ya gitta aka ce an janye shi, muna fatan Allah ya sa hakan ne ya fi alkhairi. Tabbas da an yi shi da za a samu karuwar tattalin arziki a Najeriya baki daya, ba ma kawai a harkar fim ba. Domin irin wannan masana’anta babu irin ta a kasar nan a Afirka ma irin ta daya tilo ce a kasar Afirka ta Kudu, don haka wannan abu ne na ci gaba, in da an kai ga ginata a kasar nan kana a garin Kano wacce ta shahara a harkar kasuwanci abu ne da hatta mutanen da ba su da alaka da fim za su amfana. Domin idan aka ce alkaryar fim kamar wata ma’aikata ce da za a debi masu gadi, da masu kananan aikace-aikace izuwa manyan ayyuka. Ita ma hukumar Hisba da ta tace fina-finai za ta kara samun aiki a wajen haka su ma malamai da sauran jama’a, mu dai masu shirya fina-finai za a yi domin mu ne, amma ba wajen zaman mu ba ne mu kadai. Domin mu masu yin aiki ne kawai, to ka ga wannan abu in an yi shi ba karamin gurbin samar da ayyukan yi gwamnati za ta kikira ba. Hakazalika ita ma gwamnati za ta samu kafar isar wa jama’arta sako cikin sauki sannan za ta ta samu karin kudin shiga tun daga mataki na karamar hukuma har izuwa na tarraya. To ai ka ga abu ne na cigaba ba abu ne kamar yadda wasu suka yi masa mummunar fahimta ba.
Aminiya: Maimartaba Sarkin Kano Dokta Sunusi Lamido Sunusi ya yi kira ga Gwamnati da ta duba yiwuwar ginin alkaryar fim a Jihar Kano, ko ya kuka ji da wannan kira?
dorayi: Mun yi murna kwarai, mun kuma yi farin ciki kasancewarsa babban Basarake kuma shaihin malami masanin ilimin addini da na zamani, kana uba ne ga kowa bama a Kano kawai ba. Muna alfahari dashi, in ka lura da dalilan da ya kafa maganar sa a kai, Kano ita ce tafi ko wace jiha fice a masana’artar shirya fina-finan hausa kuma ita ce cibiyar kasuwanci na Arewacin ƙasar nan dan haka ita ce ta cancanci wannan gagarumin aiki, amma idan malaman jihar suka ki yarda to sai mu haƙura a tafi da wannan kaɓakin aikin wata jihar muna kallo bayadda muka iya.
Aminiya: Me kake ganin ya sanya wadansu mutane yi wa sana’ar fim mummunar fahimta?
dorayi: To mun gode Allah wannan masana’anta ta fim ba mu ne farau ba, duniya ma ta san da wannan sana’ar kuma babu wanda bai san ana harkar fim ba. Mu dai za mu iya cewa Allah ne ya hallice mu a cikin Hausawa, kuma akwai addinin Musulunci a cikin mu, kuma shi addini ne da yake takawa duk harkar da ba ta dace ba burki, to a tunanin wasu mutane in an gina wannan katafariayar masana’anta badala za a tafka, kuma wannan abu ba haka yake ba. domin da an yi wannan aiki da hatta sukansu malaman sun samu damar da za su shiga a yi da su su tsarkake duk abin da suke ganin ana yi, wanda ya saba da addinin mu da al’adun mu, da kuma an dinga shirya fina-finan a ilmance. Misalign irin wadannan masana’antun da ake da su a kasashen da suka ci gaba za ka ga har da sashen koyar da fim din a ilimance, ta yadda ‘yan wasa za su dinga shiga aji suna daukar darasi da dai makamantan haka. Amma mu a yanzu fattan mu duk abin da ya fi alkhairi Allah ya kawo mana shi. Daman ita wannan masana’arta ba mu muka nema ba gwamnati ce ta ga ya dace ta gina.
Aminiya: Wani alfanu ka samu a wannan sana’a taka?
dorayi: To alhamdulillahi a cikinta na yi aure na hayayyafa, har na kai ga mallakar gidana da filaye nake kuma daukar dawainiyar mutanen da suke karkashina. Sannan na koya wa mutane da dama wannan sana’a a ciki da wajen Kano, to ka ga ai sai mu gode wa Allah.
Aminiya: Ko akwai wani kalubale da kuke fuskanta a wannan sana’a?
dorayi: Tabbas kowane irin aiki tafe yake da irin nashi kalubalen, musanman ma mu aikin mu da yake na jama’a, wasu suna sonka, wasu kuwa kinka suke, a haka za ka bai wa kowa hakkinsa, koda mutum ya zo mana da wani sharri ne a haka za mu hakura mu danne zuciya, mu ci gaba da aikin mu don musan sana’armu ce muke yi.