Shugaban NUC ya ajiye mukaminsa, zai koma koyarwa a BUK

Ya ce zai koma BUK ya ci gaba da koyarwa

Shugaban NUC ya ajiye mukaminsa, zai koma koyarwa a BUK

Abubakar Rasheed

Shugaban Hukumar Kula da Jami’o’i ta Kasa (NUC) Farfesa Abubakar Adamu Rasheed, ya ajiye mukaminsa da kasin kansa.

Ya bayyana hakan ne a wata hirarsa da jaridar Punch ranar, inda ya ce zai koma ya ci gaba da koyarwarsa a Jami’ar Bayero da ke Kano.

Aminiya ta rawaito cewa tsohon Shugaban Kasa Muhammadu Buhari ne ya nada Rasheed a shekara ta 2015.

An nada shi ne lokacin da Adamu Adamu yake Ministan Ilimi.

Najeriya dai ta sami yawan jami’o’i masu zaman kansu fiye da koyaushe a tarihi lokacin da Rasheed yake shugabancin NUC.

Sai dai an fuskanci yawan yajin aikin malamai da sauran ma’aikatan jami’o’i fiye da kowanne lokaci.

Kafin nadin nasa dai a 2015, ya shugabanci Jami’ar ta Bayero da ke Kano.