Shugaban PDP na Bayelsa ya rasu bayan ya koma APC
Tsohon Shugaban Jam’iyyar PDP a Jihar Bayelsa, Mista Sam Inokoba ya rasu mako biyu da komawarsa Jam’iyyar APC.A shekaranjiya Laraba ne aka bayyana rasuwar Mista Inokoba mai shekara 68 a birnin Legas kamar yadda jaridar The Nation ta ruwaito.Babu tabbaci kan abin da ya yi sanadiyyar mutuwarsa, sai dai akwai wadanda suke zargin an sanya […]
Tsohon Shugaban Jam’iyyar PDP a Jihar Bayelsa, Mista Sam Inokoba ya rasu mako biyu da komawarsa Jam’iyyar APC.
A shekaranjiya Laraba ne aka bayyana rasuwar Mista Inokoba mai shekara 68 a birnin Legas kamar yadda jaridar The Nation ta ruwaito.
Babu tabbaci kan abin da ya yi sanadiyyar mutuwarsa, sai dai akwai wadanda suke zargin an sanya masa guba ne a abinci, yayin da wasu suka ce ya hadu da ciwon zuciya ne.
Wata majiya ta ce an rika nuna tsoro kan lafiyar Inokoba wanda Kanar din soja ne mai ritaya, bayan da aka baza jita-jitar cewa ya fadi a wajen wani taron ganawa da jama’a a kauyen Nembe da ke Jihar Bayelsa a ranar 22 ga Agustan da ya gabata.
An ba da rahoton cewa an ajiye gawarsa a dakin adana gawarwaki na Asibitin Sojoji da ke Ikeja a Jihar Legas.
Tsohon Shugaban na Jam’iyyar PDP ya koma APC ne mako biyu da suka gabata tare da wasu jiga-jigan PDP kuma an sa rai ya fito takarar a zaben Gwamnan Jihar da za a gudanar a ranar 5 ga watan Disamba mai zuwa a karkashin Jam’iyyar APC.
Shi da jiga-jigan na PDP da suka koma APC, sun koma ne tare da mutum 1,150.
Sauran manyan PDP da suka koma APC tare da marigayin sun hada da tsohon Mataimakin Gwamnan Jihar Bayelsa Mista Wenirepe Seibarogu da Mista Timi Alaibe, tsohon Manajan Daraktan Hukumar Bunkasa yankin Neja-Delta (NDDC) da Sanata Heineken Lokpobiri da tsohon dan Majalisar Tarayya Mista Nadu Karibo.
Kuma Shugaban Jam’iyyar APC na kasa Mista John Oyegun ne ya karbe su zuwa jam’iyyar a wani gangani da aka gudanar a Yenagoa, babban birnin jihar.