Shugaban PDP ya ce ba adalci a jam’iyyarsu
Shugaban Jam’iyyar PDP mai mulkin Najeriya, Alhaji Ahmadu Adamu Mu’azu ya ce babu adalci a cikin jam’iyyar. Alhaji Ahmadu Mu’azu, wanda ya bayyana haka lokacin kaddamar da takarar Shugaban kasa Dokta Goodluck Jonathan a Abuja ranar Talata, ya ce hakan ne ya sa ’yan jam’iyyar da dama suka fice daga cikinta, suka koma Jam’iyyar APC.Ya […]
Shugaban Jam’iyyar PDP mai mulkin Najeriya, Alhaji Ahmadu Adamu Mu’azu ya ce babu adalci a cikin jam’iyyar.
Alhaji Ahmadu Mu’azu, wanda ya bayyana haka lokacin kaddamar da takarar Shugaban kasa Dokta Goodluck Jonathan a Abuja ranar Talata, ya ce hakan ne ya sa ’yan jam’iyyar da dama suka fice daga cikinta, suka koma Jam’iyyar APC.
Ya ce, “Babu adalci da raba daidai a PDP. Abin da ke faruwa a jam’iyyar shi ne “Kura ke shan bugu, gardi na kwace kudi. Ina so idan an ci zabe a daina yin haka.”
Alhaji Ahmadu Mu’azu ya bukaci mambobin kwamitin yakin neman zaben Shugaba Goodluck Jonathan su jajirce wajen ganin jam’iyyar ta lashe zaben 2015.
A cikin ’yan shekaru nan daruruwan ’ya’yan Jam’iyyar PDP sun fice daga cikinta saboda abin da suka kira rashin adalci.
Daga cikin fitattun wadanda suka fice daga Jam’iyyar PDP din akwai tsohon Mataimakin Shugaban kasa Atiku Abubakar da gwamnonin jihohin Kano da Kwara da Sakkwato da Ribas, Injiniya Rabi’u Musa Kwankwanso da Abdulfatah Ahmed da Aliyu Magatakarda Wamakko da Cif Rotimi Amaechi da Shugaban Majalisar Tarayya, Alhaji Aminu Waziri Tambuwal da sanatocin da suka hada da Sanata danjuma Goje da Sanata Abdullahi Adamu da Sanata Barnabas Gemade da sauransu da dama.