Shugaban Senegal ya zama sabon shugaban ECOWAS
Faye ya karɓi ragamar jagorancin ƙungiyar daga Shugaban Saliyo, Julius Maada Bio.
Bassirou Diomaye Faye
An zaɓi Shugaban Senegal, Bassirou Diomaye Faye, a matsayin sabon shugaban Ƙungiyar Raya Tattalin Arzikin Ƙasashen Yammacin Afirka (ECOWAS).
An cimma matsayar ne a Taro na 69 na Shugabannin Ƙasashe da Gwamnatocin ECOWAS da aka gudanar a Freetown, babban birnin Saliyo, inda shugabannin ƙasashen ƙungiyar suka amince da zaɓensa.
Faye ya karɓi ragamar jagorancin ƙungiyar daga Shugaban Saliyo, Julius Maada Bio.
Ana sa ran sabon shugaban ECOWAS zai jagoranci ƙoƙarin ƙarfafa haɗin kan ƙasashen yankin, inganta zaman lafiya da tsaro, da kuma bunƙasa haɗin gwiwar tattalin arziki a faɗin Yammacin Afirka.
Shugabannin ƙasashe da gwamnatoci na Ƙungiyar ECOWAS sun rattaba hannu kan wata yarjejeniya da ta amince da gina bututun iskar gas daga Najeriya har zuwa ƙasar Morocco.
Bututun iskar gas din mai nisan akalla kilomita 6,000 zai ratsa ta ƙasashe 13 da ke gabar Tekun Atlantika a nahiyar Afirka.
Kazalika, bututun zai ɗauki iskar gas daga Najeriya zuwa Morocco, inda daga nan za a tunkuda shi ta bututun yankin Maghreb zuwa kasuwannin iskar gas din a kasuwannin Turai.
Shugaban ECOWAS mai barin gado, Julius Maada Bio, shi ne ya tabbatar da cimma yarjejeniyar shimfida bututun iskar gas din daga Najeriya zuwa Morocco.