Shugaban Senegal zai cika wa’adin shekara 7

Shugaban kasar Senegal Macky Sall zai ci gaba da rike mukaminsa har zuwa shekarar 2019, sakamakon hukuncin da kotun tsarin mulkin kasar ta yanke, wanda ya bukaci shi da ya cike shekaru bakwai da aka zabe shi a maimakon yadda yake son yi wato ya sauka bayan ya cika shekaru biyar a kan karagar mulki.A […]

Shugaban Senegal zai cika wa’adin shekara 7
Shugaban Senegal zai cika wa’adin shekara 7

Shugaban kasar Senegal Macky Sall zai ci gaba da rike mukaminsa har zuwa shekarar 2019, sakamakon hukuncin da kotun tsarin mulkin kasar ta yanke, wanda ya bukaci shi da ya cike shekaru bakwai da aka zabe shi a maimakon yadda yake son yi wato ya sauka bayan ya cika shekaru biyar a kan karagar mulki.
A jawabin da ya gabatarwa al’ummar kasar ranar Talata, Shugaban ya ce zai mutunta hukuncin kotun tsarin mulkin, wadda ta ce wajibi sai ya cika shekara bakwai saboda a kan wannan wa’adin ne al’umma ta zabe shi amma ba shekara biyar ba.
Sai dai duk da cewa shugaban ya amince ya rike matsayinsa har zuwa shekara ta 2019, to amma ya bayyana 20 ga watan Maris mai zuwa a matsayin ranar da za a gudanar da kuri’ar raba gardama a game da yi wa kudin tsarin mulkin kasar gyaran fuska domin rage yawan shekarun da shugaba zai share a kan karagar mulki nan gaba, kamar yadda kafar yada labarai ta RFI ta bayyana.
A shekarar 2012 ne al’ummar kasar ta zabi Mista Sall domin tafiyar da mulki na tsawon shekara bakwai, to sai dai a shekarar da ta gabata ya bayyana aniyyarsa ta rage wa’adin mulkin zuwa shekara biyar, matakin da wasu daga cikin magoya bayansa da kuma ’yan hamayyarsa suka nuna rashin amincewarsu da shi.
A yanzu dai ko da jama’ar kasar sun amince da yi wa kundin tsarin mulkin kasar gyara fuska domin rage yawan shekarun, to dole ne shugaban sai ya ci gaba da rike matsayinsa har zuwa shekarar 2019.