Shugaban Senegal zai rage wa’adin mulkinsa
A yayin da galibin shugabannin kasashen Afirka ke kokarin canja tsarin mulkin kasashensu domin su kara wa’adin mulkinsu, Shugaban kasar Senegal Macky Sally a ba da mamamki inda ya yi alkawarin kira kuri’ar jin ra’ayin jama’a domin rage wa’adin mulkinsa daga shekara bakwai zuwa shekara biyar. Macky Sall ya sha alwashin soke karin shekaraun da […]
A yayin da galibin shugabannin kasashen Afirka ke kokarin canja tsarin mulkin kasashensu domin su kara wa’adin mulkinsu, Shugaban kasar Senegal Macky Sally a ba da mamamki inda ya yi alkawarin kira kuri’ar jin ra’ayin jama’a domin rage wa’adin mulkinsa daga shekara bakwai zuwa shekara biyar.
Macky Sall ya sha alwashin soke karin shekaraun da magabacinsa ya yi zuwa shekara bakwai, “Duk da cewa an zabe ni in yi mulki na shekara bakwai,” kamar yadda ya shaida wa masu saurarensa a Cibiyar Siyasa ta Jami’ar Harbard da ke Amurka a makon jiya.
Jawabin wanda ya gudana cikin harsunan Ingilishi da Faransanci ya ce alkawarin “yana da dalili mai kyau a yi shi ciki gagawa da sauri.”
kasar Senegal ta nuna misali abin koyi a tsakanin kasashen Afirka da suke fama da rashin gaskiya wajen rikon amana a wajen shugabanci a ’yan shekarun nan.
A bara Senegal ta kafa abin misali wajen kare turakun dimokuradiyya a daidai lokacin da takwarorinta ke kokarin yi wa dimokuradiyyar karan-tsaye, inda ta dakile yunkurin da tsohon Shugaban kasar Abdoulaye Wade mai shekara 85 cimma burinsa na tazarce karo na uku tare da kokarin dasa dansa don ya gaje shi a mulki.
Masu jefa kuri’a sun yi bore kan wannan yunkuri, inda bayan haka suka zabi Sall wani dan siyasa da yah ade kan ’yan adawa da suke yaki da cin hanci da rashawa ya zama Shugaban kasa.
Wade ya amince da shan kaye lamarin da ya jawo masa yabo, inda ya mika mulki ga Sall.
Senegal da ke fama da talauci da karuwar macewar jama’a suna da kuruciya ta fara cin gajiyar daidaiton al’amuran siyasa da dimokuradiyya a kasarta. Wannan mataki yana iya zama abin koyi ga kasashen Afirka da sauran kasahen duniya don tabbatar da ci gaban kasashen.