Shugaban Siriya ya zargi Saudiyya da tallafa wa kungiyar ISIS
Shugaban kasar Siriya Bashir al-Assad ya zargi kasashe uku da taimaka wa kungiyar ISIS, cikinsu har da kasar Saudiyya. Shugaban wanda ya musanta zargin da ake yi masa cewa Siriya ce ke mara wa ’yan ta’addan baya, ya kara da cewa sauran kasashen da ke goyon bayan IS su ne Turkiyya da kuma katar.Assad ya […]
Shugaban kasar Siriya Bashir al-Assad ya zargi kasashe uku da taimaka wa kungiyar ISIS, cikinsu har da kasar Saudiyya.
Shugaban wanda ya musanta zargin da ake yi masa cewa Siriya ce ke mara wa ’yan ta’addan baya, ya kara da cewa sauran kasashen da ke goyon bayan IS su ne Turkiyya da kuma katar.
Assad ya yi wannan zargi ne a hirarsa da wani gidan talabijin na kasar Italiya shekaranjiya.
Har ila yau, ya ce ba za a yi zabe a kasar ba tukuna saboda wani bangaren kasar yana hannun mayakan kungiyar.
Kodayake, ranar Litinin da ta gabata ne kuma Shugaban Rasha bladimir Putin ya zargi wasu kasashe 40 da bai wa kungiyar ISIS taimakon kudi ciki har da wasu kasashen da suka cikin kungiyar kasashe 20 Masu karfin Tattalin Arzikia Duniya.
A karshe ya ce wadannan kasashe yakamata su daina ba kungiyar goyon bayansu kuma su dakile cinikin danyen man fetur da kungiyar take samun kudin shiga da shi. Sai dai shugaban bai bayyana sunayen kasashen da yake zargi ba.