Shugaban sojojin haya na Wagner ya rasu a hatsarin jirgin sama

Wagner na zargin sojojin Rasha ne suka ɓaro jirgin da Yevgeny Prigozhin yake ciki

Shugaban sojojin haya na Wagner ya rasu a hatsarin jirgin sama

Gwamnatin Rasha ta tabbatar da rasuwar Shugaban sojojin haya na Wagner, Yevgeny Prigozhin a hatsarin jirgin sama.

Yevgeny Prigozhin yana cikin fasinjoji 10 da ke cikin jirginsa, wanda ya yi hatsari ranar Laraba a yankin Tver mai nisan kilomita 60 daga birnin Moscow.

Kamfanin Sojin Hayar na Wagner dai ya yi zargin cewa sojojin Rasha masu tsaron sararin samaniya ne suka kakkaɓo jirgin da Prigozhin ke ciki da wasu mutum tara.

Yevgeny Prigozhin shi ne mutumin da ya jagoranci wasu sojoji suka yi wa Gwamnatin Shugaba Vladimir Putin tawaye a cikin watan Yunin da ya gabata.

Rasuwarsa na zuwa ne a yayin da kamfanin ke kara samun gindin zama a ƙasashen yankin Sahel mai fama da mayaƙa masu iƙirarin jihadi.

Gwamnatocin sojoji da suka yi juyin mulki a yankin na ƙulla ƙawance da kamfanin Wagner domin murƙushe ayyukan ta’addanci da suke bayyanawa ci gabansu a matsayin dalilinsu na ƙwace daga hannun farar hula.

A baya-bayan nan an ga dakarun Wagner a jamhuriyar Nijar da sojoji suka yi juyin mulki suka kuma buƙaci dakarun Faransa da Amurka su bar musu kasa.

Bore da sojojin Rasha da Yevgeny Prigozhin ya jagoranta wata biyu da suka gabata ya ɗauki hankula a ciki da wajen Rasha, inda Shugaba Putin ya bayyana Prigozhin a matsayin maciyin amanar ƙasa.

Amma daga bisani suka cimma wata yarjejeniya da ta tilasta wa Mista Prigozhin yin gudun hijira zuwa ƙasar Belarus.

A cikin wannan makon ne kuma wani bidiyo ya nuna shi a yankin Sahel a nahiyar Afrika a daidai lokacin da rahotanni ke nuna cewa kamfanin Wagner ta fara ɗaukar sojoji daga nahiyar ta Afrika.