Shugaban Sri Lanka ya rantsar da Fira Minista da ministoci 18

Shugaban kasar Sri Lanka, Ranil Wickremesinghe, ya rantsar da sabon Firai Minista da kuma sabbin ministoci 18 a ranar juma’a.

Shugaban Sri Lanka ya rantsar da Fira Minista da ministoci 18

Shugaban Rikon Sri Lanka, Wickremesinghe

Shugaban kasar Sri Lanka, Ranil Wickremesinghe, ya rantsar da sabon Firai Minista da kuma sabbin ministoci 18 a ranar juma’a.

Rantsarwar ta biyo bayan cin zaben shugaban wanda majalisar kasar ta gudanar a ranar 20 ga watan Yulin da muke ciki.

An gudnar da zaben ne bayan tsohon shugaban kasar, Gotabaya Rajapaksa ya ajiye ragamar mulkin kasar.

Rahotanni sun bayyana cewa an jibge dubban jam’ian tsaro a gaban ofishin Fira Ministan inda aka rantsar da ministocin domin dakile wani abu da ka iya kawo katsalandan.