Shugaban Sudan ta Kudu ya mika wuya

A shekaranjiya Laraba ne kasar Shugaban Sudan ta Kudu, Salba Kiir ya sanya hannu a kan wata yarjejeniyar zaman lafiya tare da ‘yan tawayen kasar, kamar yadda BBC ta ruwaito.Yarjejeniyar za ta share fagen kafa gwamnatin hadin kan kasa tare da shugaban ‘yan tawaye, Riek Machar.Tun da farko dai jagoran ‘yan tawayen kasar, Riek Machar, […]

Shugaban Sudan ta Kudu ya mika wuya
Shugaban Sudan ta Kudu ya mika wuya

A shekaranjiya Laraba ne kasar Shugaban Sudan ta Kudu, Salba Kiir ya sanya hannu a kan wata yarjejeniyar zaman lafiya tare da ‘yan tawayen kasar, kamar yadda BBC ta ruwaito.
Yarjejeniyar za ta share fagen kafa gwamnatin hadin kan kasa tare da shugaban ‘yan tawaye, Riek Machar.
Tun da farko dai jagoran ‘yan tawayen kasar, Riek Machar, ya sanya hannu a kan yarjejeniyar a makon da ya wuce.
Shugabannin kasashen yankin kamarsu Shugaban Kenya Uhuru Kenyatta  da Yoweri Musabeni na Uganda, da kuma Hailemariam Desalegn na kasar Habasha sun shaida sa nya hannu a kan yarjejeniyar a birnin Juba na Sudan ta Kudu. Yarjejeniyar dai tana nufin dawo da zaman lafiya da kwanciyar hankali. Har ila yau, ana fatan Mista Kiir zai dawo da mataimakinsa Riek Machar kujerarsa ta mataimakin shugaban kasa bayan korarsa da ya yi.
Wakilin BBC a birnin Juba ya ce kafin Mista Kiir ya sanya hannu a yarjejeniyar, sai da ya shafe lokaci mai tsawo yana tattaunawa da shugabannin kasashen yankin asirce.
A shekarar 2011, Sudan ta Kudu ta samu ‘yan cin kai, amma ba da jimawa ba kasar ta auka cikin mummunan yakin basasa a shekarar 2013.
Fada tsakanin magoya bayan bangarorin biyu ya raba mutane fiye da miliyan biyu da muhallinsu da dama kuma suka rasa rayukansu.