Shugaban Sudan ya dauki matakan tattaunawa da ‘yan adawar kasar

Shugaban kasar Sudan Umar al-Bashir ya ba da umarnin sakin fursinonin siyasar da ke tsare da kuma sassaucin takura da ake wa ‘yan adawa kasar, a wani mataki da yake ganin zai taimaka don samun nasarar shirinsa na shigo da ‘yan adawar kasar wani shirin tattaunawa da gwamnatinsa. Da yake jawabi ranar Lahadin da ta […]

Shugaban Sudan ya dauki matakan tattaunawa da ‘yan adawar kasar
Shugaban Sudan ya dauki matakan tattaunawa da ‘yan adawar kasar

Shugaban kasar Sudan Umar al-Bashir ya ba da umarnin sakin fursinonin siyasar da ke tsare da kuma sassaucin takura da ake wa ‘yan adawa kasar, a wani mataki da yake ganin zai taimaka don samun nasarar shirinsa na shigo da ‘yan adawar kasar wani shirin tattaunawa da gwamnatinsa.
Da yake jawabi ranar Lahadin da ta gabata a lokacin fara shirin tattaunawar, ya ce zai fara ne da sasanta wa da shugabannin jam’iyyun siyasar kasar fiye da 50. Daga bisani kuma zai masu tayin shiga shirin tattaunawar. Ya kuma ba da tabbacin cewa zai cire duk wasu takura da yake wa ‘yan jarida kasar.
Shugaba al-Bashir ya kara da cewa: “Dalilin faro wannan tattaunawar shi ne don samun kyakkyawar fahimta tsakanin mu da jam’iyyun adawar kasar nan wanda hakan zai tabbatar da wanzuwar zaman lafiya a duk fadin kasar nan. Na umarci dukkannin hukumomin da ke kasar nan da su sakar wa dukkannin jam’iyyun siyasar da muke da su mara ba tare da wani shamaki ba, in har hakan bai saba wa dokar kasa ba”
Ya ci gaba da cewa “ na ba da umarnin sakin dukkannin fursinonin siyasa da ke tsare amma banda wadan da ake tuhumar su da aikata manyan laifuffuka” Inji shi
Shugaban  Jam’iyyar  adawa ta Umma, Sadik al- Mahdi ya yi maraba da matakin gwamnatin. Amma Shugaban jam’iyyar  Popular Congress, Hassan al-Turabi ya bayyana cewa zai so a ce wandan da zasu jagoranci tattaunawar su kasance mutane ne da kowa ya aminta da adalcinsu.
Sai dai ra’ayin wasu gamayyar jam’iyyun kasar su 17 ya sha ban-ban, inda suka ce ba za su yi na’am da matakan gwamnatin ba har sai ta cika dukkkannin sha’ruddan da suka gindaya mata.
A cikin watan Janairun da ya wuce ne dai, gamayyar jam’iyyun suka gindaya ya sharuddan inda suka bukaci: soke duk wata doka da ta hana jama’a bayyana ‘yancinsu da kuma kawo karshen rikice-rikicen cikin gida da kasar ke fama da su da sakin dukkannin fursinonin siyasa, sai kuma bukatarsu ta Shugaba al-Bashir ya sauka daga mulki kuma ya mika wa gwamnatin rikon kwarya wanda zata jagoranci zaben sabuwar gwamnatin a kasar.