Shugaban Sudan ya yi layar zana a taron Afirka na Abuja

Shugaban kasar Sudan Omar Hassan Al-Bashir ya yi layar zana a wurin taron Abuja+12, wanda wani taron bin diddigi ne kan Babban Taro a kan Cututtukan kanjamau da Tarin Fuka da Maleriya da sauransu, sakamakon kiraye-kirayen da kasashen Turai da wasu kungiyoyin kare hakkin dan Adam na Najeriya suka yi na a kama shi. Kotun […]

Shugaban Sudan ya yi layar zana a taron Afirka na Abuja

Sudan’s President Omar al-Bashir reviews the troops as he arrives at the Nnamdi Azikiwe International Airport in Abuja on July 14, 2013 to take part in a African Union summit about HIV, TB and malaria. Nigeria is a member of The Hague-based International Criminal Court, which in 2009 and 2010 issued two warrants against Bashir […]

Al- Bashir lokacin da ya zo NajeriyaShugaban kasar Sudan Omar Hassan Al-Bashir ya yi layar zana a wurin taron Abuja+12, wanda wani taron bin diddigi ne kan Babban Taro a kan Cututtukan kanjamau da Tarin Fuka da Maleriya da sauransu, sakamakon kiraye-kirayen da kasashen Turai da wasu kungiyoyin kare hakkin dan Adam na Najeriya suka yi na a kama shi.
Kotun Duniya (ICC) ta ba da warantin kama Shugaba Al-Bashri ne a shekarar 2009 da 2010 kan zarginsa da hannu a rikicin yankin Darfur da ke Sudan, inda aka zargi sojojin gwamnati da Larabawa masu dauke da makamai da hada hannu wajen yakar ’yan tawayen yankin, wadanda galibinsu bakaken fata ne.
Al-Bashir, wanda ya iso Abuja a ranar Lahadi kuma ya samu tarbar girmamawa, ciki har da faretin soja, ya kaurace wa taron, wanda aka sa rai zai halarta tare da sauran shugabannin kasashen Afirka. Lokacin da aka nemi ya zo ya gabatar da jawabinsa, sai wurin ya yi tsit ba tare da ya bayyana ba.
Wata majiya ta shaida wa wata kafar labarai cewa Shugaba Al-Bashir ya sulale daga wurin taron ne saboda tsoron kada kasashen Turai su shammace shi su yi amfani da wannan dama su kame shi, inda majiyar ta ce ya bar Najeriya ne a wanshekare ranar Litinin.
Wata majiya a ofishin Jakadancin Sudan ta tabbatar wa kafar labaran cewa Shugaban na Sudan ya bar Najeriya a yammacin Litinin. Kuma ba a ga Shugaba Al-Bashir a wajen liyafar cin abinci da Shugaba Jonathan ya shirya wa shugabannin Afirka a ranar Litinin din ba.
Rikicin Darfur dai ya jawo mutuwar dubban mutane, kuma tun bayan umarnin kotun na a kama Shugaba Al-Bashir aka hana shi zuwa kasashen Uganda da Afirka ta Kudu da Malawi da kuma Zambiya, yayin da Chad da Djibouti ne kawai suka karbi bakuncinsa a bara. Zuwansa Najeriya shi ne karo na farko a Afirka ta Yamma, tun bayan umarnin kama shi.
kungiyar Tarayyar Afirka (AU), wadda ta shirya taron ta sha sukar umarnin kotun duniyar, inda ta ce ba za ta girmama hukuncin kotun ba.
A shekarar 2010, kungiyar AU ta bukaci Kwamitin Sulhu na Majalisar dinkin Duniyya kan ya dakatar da shari’ar zargin Shugaban na Sudan da aikata miyagun laifuffuka.
A ranar Litinin Najeriya ta bayyana cewa ba za ta mika Shugaba Al-Bashir ga kotun ba, inda kakakin Shugaban kasa, Dokta Reuben Abati ya ce Al-Bashir yana halartar taron ne kamar sauran shugabannin Tarayyar Afirka ba kuma dole ne ya zamo bisa gayyatar Najeriya ba.
An ruwaito shi yana cewa:  “Najeriya tana daukar nauyin taron ne kawai, ba ita ta gayyace shi ba, don haka Najeriya ba ta da ikon ta yanke shawarar wa zai halarci taron AU, wane ne ba zai halarta ba.”
Wata kungiya mai suna Socio-Economic Rights and Accountability Project (SERAP) na cikin kungiyoyin da suka nemi a kama Shugaba Al-Bashir kamar yadda Babban Daraktanta Adetokunbo Mumuni, ya fadi a cikin wata sanarwa.
Domin tabbatar da an samu nasarar rigakafi da jinya da kula da kuma tallafa wa dukkan ’yan Najeriya da ke dauke da cuttar kanjamau, Shugaba Jonathan da Shugaban AU kuma Firayiministan kasar Habasha Mista Hailemariam Dessalegn, sun kaddamar da wani gamammen shiri mai suna Comprehensibe Response Plan (PCRP).   
Jonathan da sauran shugabannin Afirka da kungiyar AU da kuma Majalisar dinkin Duniya, sun ce wajibi ne yankin Afirka ya rage dogaro da tallafin kasashen waje da kuma shigo da wadatattun magungunan da ake bukata don magance cututtukan. Sannan taron ya amince da kudirin kafa Cibiyar Yaki da Cututtuka ta Afirka.
Shugaba Jonathan ya kara da cewa “… a lokaci mai tsawo, rashin daidaiton harkokin siyasa da rashin tsaro da cututtuka masu yaduwa sun zame tarnaki ga kokarinmu na ci gaba da kuma sarrafa dimbin albarkatun da suke jibge a yankinmu. Amma a yau mun sake jaddada fata, cewa hada hannu tare da kuma amfani da dabarunmu na gida za mu iya magance wadannan matsaloli baki daya.”
Babban Sakataren Majalisar dinkin Duniya Mista Ban Ki-Moon wanda Babban Daraktan Hukumar Kula da Yawan Jama’a ta Majalisar (UNDP) Farfesa Babatunde Osotimehin ya wakilta, ya ce, a kowane minti daya yaro daya kan mace a Afirka saboda cutar maleriya, yayin da kowane mutum daya daga cikin 20 a yankin ke dauke da cutar kanjamau ko tarin fuka, wanda shi ne mafi yawa a tsakanin yankunan duniya.