Shugaban Taliban Mullah Omar ya rasuShugaban Taliban Mullah Omar ya rasu
Wasu majiyoyin gwamnatin kasar Afghanistan sun ce shugaban kungiyar Taliban Mullah Omar, ya rasu. Gidan rediyon BBC da ya bayar da labarin ya ce sai dai kungiyar ba ta ce komai a kan wannan ikirari da majiyoyin suka yi ba.Majiyoyi daga hukumar leken asirin kasar sun ce Mullah Omar ya rasu ne shekara biyu zuwa […]
Wasu majiyoyin gwamnatin kasar Afghanistan sun ce shugaban kungiyar Taliban Mullah Omar, ya rasu.
Gidan rediyon BBC da ya bayar da labarin ya ce sai dai kungiyar ba ta ce komai a kan wannan ikirari da majiyoyin suka yi ba.
Majiyoyi daga hukumar leken asirin kasar sun ce Mullah Omar ya rasu ne shekara biyu zuwa uku da suka wuce.
Kuma ba a bayar da cikakken bayani a kan dalilin mutuwarsa.
Wani mai magana da yawun kungiyar ta Taliban da BBC ya tuntuba ya ce nan gaba kadan ne za su fitar da sanarwa a kan batun.
A baya dai an sha bayar da rahotannin da ke cewa Mullah Omar ya rasu.
Wannan shi ne karon farko da hukumomin kasar ke tabbatar da rasuwarsa.
Mullah Omar shi ne ya jagoranci Taliban wajen yin nasara a kan kungiyoyi masu hamayya da su a yakin basasar da ya faru bayan janye dakarun Tarayyar Sobiyet daga kasar.
kawancen da ya kulla da shugaban kungiyar Alka’eda Osama Bin Laden ne ya sa Amurka ta jagoranci mamayar da aka yi wa Afghanistan a shekarar 2001, bayan harin da aka kai a biranen New York da Washington a ranar 11 ga watan Satumban shekarar.
Amurka ta sa diyyar Dala miliyan10 (kimanin Naira biliyan biyu da miliyan 300) ga duk wanda ya taimaka ta kama Mullah Omar, kuma tun daga lokacin ne ya rika buya.
’Yan Taliban sun kwashe shekaru suna fitar da sakonnin da suka cewa sun fito ne daga Mullah Omar, inda a lokacin bukukuwan karamar Sallah aka fitar da wani sako da ke cewa Mullah Omar ya nuna goyon bayansa ga shirin tattaunawar sulhu da gwamnatin Afghanistan. Sai dai bai ce komai a kan ganawar da ya yi a hukumance da wakilan gwamnatin Afghanistan mako daya kafin nan ba, wadda kasar Pakistan ta jagoranta.