Shugaban Tanzania John Magufuli ya rasu

Shugaban Kasar Tanzania John Pombe Magufuli ya riga mu gidan gaskiya. Mataimakiyarsa, Samia Suluhu ce ta sanar da rasuwar Mista Magufuli a kafar yada labaran kasar. Ahmad Lawan ya roki Saudiyya ta sako ’yan Najeriya 10,000 da ta tsare ’Yan bindiga na samun taimako daga kasashen waje —NSCDC Magufuli ya rasu a ranar Laraba a […]

Shugaban Tanzania John Magufuli ya rasu

John Pombe Magufuli

Shugaban Kasar Tanzania John Pombe Magufuli ya riga mu gidan gaskiya.

Mataimakiyarsa, Samia Suluhu ce ta sanar da rasuwar Mista Magufuli a kafar yada labaran kasar.

Magufuli ya rasu a ranar Laraba a wani asibiti Dar es Salaam, babban birnin kasar inda ya  yi jinya ta ciwon zuciya.

Saluhu ta ce a ranar 14 ga watan Maris ne jikin shugaban ya yi tsanani inda kuma aka kwantar da shi a asibiti.

Rahotanni sun bayyana cewa ya shafe fiye da shekara 10 yana fama da larurar.

Magufuli ya bar duniya yana da shekaru 61.

Boko Haram sun ƙone makarantu a Borno

Har yanzu ’yan bindiga ba su saki matar Manjo Janar Rabe ba

An binne gawar Manjo Janar Rabe a Katsina

Wasu tsiraru ne ke rura matsalar tsaro a Najeriya — Christopher Musa